✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan kula da zaman lafiya da tsaro a zamanina – Farfesa Bande

Wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya kuma Shugaba mai jiran gado na Babban Zauren Majalisar kashi na 74. Farfesa Tijjani Muhammad Bande ya…

Wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya kuma Shugaba mai jiran gado na Babban Zauren Majalisar kashi na 74. Farfesa Tijjani Muhammad Bande ya ce zai mayar da hankali ga tafiyar da tsarin ci gaba na bai-daya da harkar zama lafiya da kuma tsaro.

Da yake magana a yayin wata ziyara da ya kawo hedikwatar jaridar Daily Trust Abuja a ranar Litinin, Farfesa Bande ya ce “Wadansu na tambayar wane sabon abu zan kawo? Abubuwan da zan kawo sun kunshi maganar zama lafiya da tsaro a duniya. Ka san Afirka ce gaba daya ta tsayar da ni na yi takara kuma sauran kasashe suka aminta da ni, kuma duk wani abu da ya shafi Afirka ya shafi sauran kasashe don haka zan mayar da hankali wajen kawo ci gaba na bai- daya.”

Da yake tsokaci kan dambarwar rashin tsaro a kasashen Gabas ta Tsakiya da tashe-tashen hankula da suke faruwa a kasar Libiya, cewa ya yi “Ka san yaki ba abu ne mai kyau ba, ga shi kuma akwai matsaloli a nahiyarmu. Don haka dawo da zaman lafiya a kasar Libiya muhimmin abu ne a gare mu.”

Ya yi karin bayani game da gidauniyar da majalisar ta kafa don samar da zunzurutun kudi Dala biliyan 50 don yashewa da farfado da Tafkin Chadi. “Shugaba Buhari ya karfafa batun Tafkin Chadi kuma ya yi mana bayanin irin mummunan halin da wannan tafki ya fada da kuma yadda hakan ya haifar da matsalar tsaro saboda yadda mutane da dama a Najeriya da wasu kasashe suka fada cikin mawuyacin hali saboda rasa hanyoyin neman abincinsu,” inji shi.