✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan sauya matsaya kan makamin nukiliya – Shugaban Koriya

Shugaban Kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya ce yanzu ya dukufa kan shirin kawo karshen mallakar makamin nukiliya tare da gargadin cewa, zai sauya…

Shugaban Kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya ce yanzu ya dukufa kan shirin kawo karshen mallakar makamin nukiliya tare da gargadin cewa, zai sauya matsaya muddin Amurka ta ci gaba da kakaba musu takunkumi.

Shugaban ya furta haka ne a yayin gabatar da jawabin shiga sabuwar shekara ga al’ummar kasar a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce, matukar Amurka ba ta cika alkawuranta ba, to babu wani zabi da ya rage musu illa lalubo wata sabuwar hanyar kare ’yancin kasar.

A cikin watan Yunin bara  ne a Singapore, Kim ya gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump kan batun kwance makamin nukiliyar kasarsa, amma har yanzu babu wani gagarumin sauyi. Sakamakon da ya biyo bayan wannan ganawa da ta farfado da alakar diflomasiya a tsakaninsu.

Shugabannin biyu sun gana ne bayan Koriya ta Arewa ta gudanar da jerin gwaje-gwajen makamai masu linzami, ciki har da wanda ta ce, zai iya riskar tsakiyar Amurka, lamarin da ya zafafa musayar yawu a tsakanin kasashen biyu. Shugaba Kim ya bayyana cewa, a shirye yake ya sake wata ganawa da Trump a kowane lokaci daga yanzu.