✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan tona asirin ’yan bindiga da iyayen gidansu – Gwamnan Zamfara

A tattaunawa ta musamman da Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Mutawalle ya yi da Aminiya a fadar gwamnati da ke Gusau, ya sha alwashi tona…

A tattaunawa ta musamman da Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Mutawalle ya yi da Aminiya a fadar gwamnati da ke Gusau, ya sha alwashi tona asirin masu daukar nauyin ’yan ta’adda a jihar tare da alkawarin samar da tsaro a jihar. Ya tabo batutuwa da dama kamar yadda za a karanta:

Mai girma Gwamna ka zamo Gwamnan Jihar Zamfara kuma ka same ta a mawuyacin hali, ta ina ka fara?

A matsayina na dan Adam dole sai na duba yadda al’amura suke, musamman ta yadda tsaro ya tabarbare a jihar, in samu ainihin yadda abubuwa suke tare da tunanin yadda zan fuskance su. Ganin cewa an tabbatar mini da kujerar Gwamna ne kwana hudu kafin a rantsar da sabuwar gwamnati, wannan ya sanya ban samu lokacin da zan kafa wani kwamiti da zai duba al’amuran ba.

Mun kafa kwamiti mai karfi wanda ke tuntubar ’yan bindiga da suka addabi al’umma, haka kuma kwamitin zai tuntubi al’umma da masu rike da sarautun gargajiya, don a samu damar zama a sasanta saboda Jihar Zamfara ta samu zaman lafiya.

Akwai rade-radin da jama’a ke yi cewa gwamnatinka za ta biya diyya ga ’yan bindiga, yaya batun yake?

A duk lokacin da za ka yi magana, to mutum ya fadi gaskiya kuma kada a sanya yaudara, amma ka fada wa al’umma cewa zan samar muku da hanyoyi da asibitoci da makarantu da kuma wuraren koyar da sana’o’i amma ka ce wa al’umma za ka ba su kudi, wannan ba daidai ne ba.

Idan ka ba ’yan bindiga kudi ko masu garkuwa da mutane, ai ka kara rura wuta ce domin wadansu ma za su dauki bindiga su fara tozarta jama’a, domin su ma a ba su kudin.

Tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ya sha fadi a kafafen labarai cewa yin amfani da sulhu wajen magance ayyukan ’yan ta’adda ba zai kai ga nasara ba, kai ka na ganin haka zai yiwu?

Ai shi ba jami’in tsaro ne ba kuma bai san komai game da kalubalen tsaro ba kuma kada mu manta, duk abin da Allah Ya bayyana ai to kuskure ne mu ki aiwatarwa.

Ka dauko aikin gina filin jiragen sama a Jihar Zamfara, yaya ka dauki aikin?

Akwai rubuce-rubuce a kafafin watsa labarai a kan wannan aiki da aka yi, wanda kamata ya yi su samu cikakken bayani game da aikin gina filin jirgin, kafin su ci gaba da rubuce-rubucen da suke yi.

Wani abu da na tsara don ciyar da Jihar Zamfara gaba shi ne na bayyana cewa duk wanda ke son zuba jari a Jihar Zamfara ya zo kai-tsaye za mu yi haka ne ta hanyar shiga ’yarjejiniya. Jihar Zamfara ita ce za ta mallaki filin kamar yadda sauran jihohin Arewa suke da shi, in ka duba Jihar Zamfara ce kawai ba ta da filin jirgin sama, ko Zamfara ce ba ta son ci gaba da bunkasa tattalin arziki?

Shekara 20 da mulkin dimokuradiyya amma ba wani ci gaba da Jihar Zamfara ta samu, wannan ne ya sanya na kudiri aniyar ganin na bijiro da aikace-aikacen da za su bunkasa tattalin arzikin jihar. Zan yi duk mai yiwuwa koda kuma zan kashe dukk kudin da na mallaka a jihar don Zamfara ta ci gaba. Matsalar ba ta kudi ba ce, domin zan yi amfani da kwarewata da hikimata da basirata in samar da yanayi mai kyau da kudaden da za su shigo don gudanar da ayyukan raya Jihar Zamfara kamar samar da wadanda za su hada hannun da gwamnati ta hanyar zuba jari a jihar. Saboda na yi tafiye-tafiye da dama inda idanuwana suka bude, na tashi daga bakauye na zama wayayye, don na san yadda zan shawo kan mutane su zo su zuba jari a jihata kamar yadda na ja mutane suka zuba jarinsu a Jamhuriyar Nijar, don haka me zai hana in kawo su su zuba jari a jihata? Duk wanda yake son ya zuba jari a Jihar Zamfara zan ba shi dama dari bisa dari saboda abin da nake bukata ne.

Wane shiri ka yi wa ilimi a matsayinka na Gwamna?

A halin da ake ciki, mun samar wa dalibai 200 guraben karatu a jami’o’i a ciki da wajen Najeriya, mun rigaya mun biya kudaden karatunsu kuma mun kammala dukkan shirye-shiryen tafiyarsu saboda mu samu nasarar karatun dalibai. Na kirkiro da mai taimaka mini na musamman kan bayar da guraben karatu, wanda kuma ya cancanta kuma umarnin da na bayar shi ne a tafi cikin yankunan karkara a zakulo dalibai amma ban da ’ya’yan jami’an gwamnati da na ’yan majalisa da na masu hannu da shuni, haka nan kuma duk wanda mahaifinsa ke karbar albashi a matsayinsa na ma’aikaci to bai cancanci ya samu wannan dama ba. Saboda haka shiri ne na masu karamin karfi, na wadanda ba za su iya daukar nauyin karatunsu ba.

Zan tabbatar da ganin cewa al’ummar Jihar Zamfara sun samu ilimi kyauta, mai inganci musamman ’ya’yan talakawa.

Wani bangare shi ne harkar kiwon lafiya, inda akan samu mace-macen mata da yara musamman a yankunan karkara. Wane shiri kake da shi don fuskantar wadannan matsaloli?

Na zagaya wasu daga cikin asibitocinmu, na ga irin yadda suke cikin matsaloli kuma tuni na bayar da umarni a hanzarta samar da dukkan muhimman kayayyakin da suke bukata don ingantuwar aikin, wadanda suka hada da muhimman magunguna, wanda tuni har magungunan sun isa asibitocin.

Ina son ganin dukkan asibitocin gwamnati an samar da dukkan muhimman kayan aiki don inganta lafiyar al’umma, kamar yadda a halin yanzu akwai likitoci 29 daga kasar Koriya, inda har aka yi garkuwa da guda daya amma cikin ikon Allah sun sako shi. Hakan ne ya sanya Jakadan kasar Koriya zai ziyarci Jihar Zamfara kuma za mu shiga wasu yarjeniyoyi da kasar a lokacin ziyarar, haka kuma kasar Kyuba ta miko takardar neman a ba ta damar ta zo ta bayar da tata gudunmawa a jihar ta Zamfara.

Wani shiri kake da shi a kan almajiranci, ganin Jihar Zamfara ce ta daya wajen tura yara zuwa almajiranci?

Na kafa kwamiti na zakulo duk wani wuri da ake karatun allo, domin mu san yawansu kuma za mu gina makarantun da za su dace da zamani, wadanda za su iya daukar dalibai kamar 1,500 tare da gina gidan malamin da zai kula da makarantar. Bayan kwamitin ya gama tantancewa tare da yi wa su kansu malaman jarrabawa a kan karantarwa kafin har a amince da shi malamin.

A ayyukan raya kasa Jihar Zamfara tana baya ba kamar sauran jihohin ba. Muna kokarin mu gina daukacin hanyoyin da ke jihar, kuma da yardar Allah kafin in kammala shekaruna zan mayar da Jihar Zamfara abin koyi ga saura ta fuskokin gine-gine da samar da ingantattun hanyoyi.

wadannan.