✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi mulki tare da kowane bangare —Sarkin Zazzau

Ya ce ba laifi don wasu ’ya’yan sarauta sun nemi zama sarki

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya yi alkawarin aiki da gidajen sarautar masarautar a mulkinsa yana mai kira ga jama’arsa da su hada kai tare da zama lafiya da junansu.

Da yake jawabi bayan Gwamnatin Jihar Kaduna ta nada shi, Sarki Ahmed Bamalli ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautar domin samar da cigaba.

“Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanina da sauran gidajen Saurautar Zazzau kuma mun gaji girmama juna a matsayin ’yan uwa na jini”, inji sarkin a yayin bayyana kusancinsa da sauran gidajen saurautar masarauta na Katsinawa da Barebari a masarautar.

“Matata ’yar gidan Katsinawa ce kuma diyar marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris, kakannina na bangaren uwa kuma Barebari ne, saboda haka ba dalilin rashin jituwa tsakanin gidajen.

“Shi ya sa na zama dan gidajen biyu saboda su ne manyan gidajen Sarauta a Zazzau”.

Sarkin ya ci gaba da cewa, “Allah ke nada sarki ba dukiyata ko ilimina ko ikona ba domin da wadannan abubuwan za a duba to da ba ni zan zama saki ba.

“Allah Na ba da mulki ne ga wanda Ya ga dama a duk lokacin da Ya so saboda haka mu mayar da komai gare Shi”, inji sarkin.

Ya bayyana cewa ba laifi ba ne don wasu ’ya’yan sarauta sun nemi zama sarki domin su ma hakki su nema.

Sai dai ya jaddada muhimmancin “sauran su mara wa duk wanda ya zama sarki baya kar a wahalar da jama’a.

“Ina rokon su da su zo mu ciyar da Masarautar Zazzau gaba kuma ina fatar nan ba da dadewa ba za mu fahimci juna.

“Na ji dadin yadda wasu hakimai daga gidajen Katsinawa da Barebari suka zo suka yi min mubaya’a.

“Kowa ya zo mu yi aiki tare, ni kuma zan yi iya kokari na wajan hada kan Zazzagawa”, inji Sarki Ahmed.