Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Zan yin kwal-kwabo in Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa  – Bello ‘BMB’

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello (BMB)
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello (BMB)

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello (BMB) ya sha alwashin cewa zai yi aski kwal-kwabo idan Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa da za a gudanar a ranar Asabar din makon gobe 16 ga Fabrairu.

Jarumin ya yi wannan alwashi ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ranar Lahadin da ta gabata.

ADVERTISEMENT

Jarumin wanda ake yi wa lakabin ‘Cibilian General’ ya ce an rika yi masa tayin ba shi makudan kudade don ya aske gashin kansa amma ya ki, inda yanzu ya ce zai yi kwal-kwabo kyauta idan har Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa.

BMB wanda darakta ne kuma mai tsara labaran fim ya ce wani furodusa ya taba tayin ba shi Naira miliyan 1 da dubu 500 idan har yarda zai aske gashin kansa don ya fito a wani fim, amma ya ki saboda irin yadda yake son tara gashi a kansa.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta gano BMB yana dauke da gashin da ke kansa fiye da shekara 10 ba tare da ya yi askin kwas-kwas ko saisaye ba.

Ya ce, “Wani furodusa ya taba yi mini tayin Naira miliyan 1 da dubu 500 don in aske kaina don in fito a fim dinsa, amma na ki, amma yanzu idan har aka bayyana cewa Buhari ya lashe zabe to zan aske kaina kwal-kwabo, hakan zai nuna yadda nake son Buhari,

“Na kuma yi alkawarin haka ne don in kafa wani tarihi, da zarar an ce Buhari ya lashe zaben bana shi ke nan sai ia aske kaina kwal-kwabo. Allah Ya ba ni ikon cika alkwarin,” inji BMB.

BMB wanda ya fito a fina-finai irin su ‘Hanyar Kano’ da ‘Gwaska Ya Dawo’ da kuma ‘Don Ali’ ya bukaci ’yan Najeriya su zabi Buhari saboda salon shugabancinsa da halayensa da kuma dabi’unsa nagari da suka riga suka bayyana.