Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Zanen batanci ga Annabi: Shugabannin addini sun tanka

daukar fansa bai taso ba, a bar su da makircinsu – Sheikh Zazzaky

ADVERTISEMENT

Jagoran ’yan uwa Musulmi a Najeriya Sheikh Ibrahim Zazzaky ya ce zanen batanci da mujallar Charlei Hebdo ta yi wa Annabi Muhammadu (SAW) wani makirci ne kawai domin a tayar da hankalin Musulmin duniya saboda wata biyan bukata tasu.
Sheikh Zakzaky ya ce ya yi bayani a laccar da ya gabatar a wajen Maulidi ranar Lahadikan lamarin, amma duk da haka idan za a iya tunawa sun taba kulla irin wannan makirci a lokacin da suka kai wa cibiyar kasuwanci da ke Amurka hari a ranar 11 ga Satumba wanda har biki suke na ranar tunawa da shi kuma kowa ya san wannan makirci ne suka kulla.
Ya ce “Wadannan mutane Yahudawa da Nasara ba su da abin bauta domin su ba su da Allah kuma duk da ikirarin da Yahudawa suke yi na cewa Annabi Musa (AS) Annabinsu ne, karya ne haka ma Nasara da suke cewa Annabi Isah (AS) Manzonsu ne karya suke yi, mu ne muka yarda cewa Annabawa da Manzanni.”
Sheik Zakzaky ya ce “Idan ka ce za ka dauki fansa ko ramuwar gayya a kan wa za ka rama? A kan shugaban Yahudawa ko a kan Shugaban Faransa. Ai a duniya babu abin da za ka kwatanta shi da Manzon Allah (SAW), kuma babu abin da ya kai shi daraja a duniya don haka duk wani daukar fansa da za ka yi ba zai huce maka zuciyarka ba, don haka batun daukar fansa ma bai taso ba, a bar su da makircinsu Allah Ya ishe su.”

ADVERTISEMENT