✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar #EndSARS ta kassara Tattalin Arzikin Kasa —Minista

Gwamnatin Tarayya ta ce nakasun tattalin arziki da zanga-zangar #EndSARS ta haifar zai dauki lokaci kafin kasar ta murmure. Ministan Watsa Labarai, Lai Mohammed, ya…

Gwamnatin Tarayya ta ce nakasun tattalin arziki da zanga-zangar #EndSARS ta haifar zai dauki lokaci kafin kasar ta murmure.

Ministan Watsa Labarai, Lai Mohammed, ya bayyana hakan jim kadan bayan karbar korafe-korafen da gwamnati ta samu daga kungoyoyi masu nesanta kawunansu daga zanga-zangar da yanzu ta tasamma komawa rikici.

Lai Mohammed ya ce, kungiyoyin sun bayyana cewar an fara sauya akalar zanga-zangar domin a cimma wata manufa ta daban.

Ya ce, “Mun samu korafe-korafe daga kungiyoyi da dama da suka ce da farko sun goyi bayan zanga-zangar #EndSARS ne bisa yakinin cewar don ’yan Najeriya ake yin ta.

“Suka ce a ’yan kwanakin da suka wuce, zanga-zangar ta yi musu illa kai tsaye ta hanyar hana su zuwa wuraren aiki da kasuwa da kuma fasa wa mutane shaguna ana kwashe musu dukiyoyi.

“Yau da safe na karanta a jarida cewar daya daga cikin wadanda suka hada zanga-zangar ta #EndSARS ya ce ya janye saboda wasu sun kwace ta daga hannunsu.

“Ya bayyana cewar a yanzu suna karbar umarni ne daga kasashen waje, kuma ana turo musu kudade wanda ba shi ne manufarsu ba”, inji ministan.

Ministan ya roki masu zanga-zangar da su kawo karshenta domin su kauce wa makircin masu neman yin amfani da su wajen kawo rikici a kasar.

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta amsa duk bukatun da suka gabatar mata, kuma tuni gwamnoni suka fara aiwatar da wasu daga cikinsu.

Ya ja hankalinsu da cewar, yunkurin kashe Gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola, da kubutar da fursunoni daga gidan yari a birnin Benin tabbaci ne na cewar wasu sun kwace zanga-zangar.

Mohammed ya ce, mutane su kuma yi la’akari ida kone ofishin ’yan sanda da aka yi da kuma balle shaguna da sace-sacen dukiyoyin mutane da aka rika yi a Jihar Edo ya tilasta saka dokar ta baci.

Ministan ya kuma koka da harin da masu zanga-zangar suka kai wa ‘yan sanda masu kai taimakon gaggawa (RRT) a lokacin da suke sintiri a unguwar Lekki ta jihar Legas.

“Saboda haka ba za a ce zanga-zangar ta lumana ba ce tunda mutane na rasa rayukansu kuma ana hana yan kasa zuwa wuraren neman abincinsu.

“An hana mutane da dama motsi a bangaren Lekki na Legas, kuma gwamnati jihar ta ce tana asarar sama da Naira miliyan 200 a duk rana.

“Akwai wata mai juna biyu da aka ce ta rasa ranta sakamakon tare hanyar da aka yi na tsawon awanni kafin mutum ya isa wurin da zai je”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa zanga-zangar da matsalolin COVID-19 da kasa ta shiga sun kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar da zai bukaci lokaci kafin a fargado.

Amma ya ce duk da haka gwamnati za ta cigaba ta kulawa da bukatun matasa, sai dai kuma ba za ta zura ido a rika cutar da rayuwar al’ummar kasa ba.

“Gwamnati na da hakkin tabbata da doka da oda, zaman lafiya da kuma ba wa mutane damar neman abincinsu cikin lumana; Gwamnati ba za ta zura ido a jefa kasa cikin fitina ba.

“Durkusa wa wada ba gajiyawa ba ne na ganin mun biya wa masu zanga-zangar bukatunsu, amma kuma ba zamu manta da hakkinmu ba na sauyke nauyin da ke kanmu na kare kas aba”, inji shi.

Ya kara da cewar gwamnati ba za ta yarda tsirarun mutanen da ke da wata boyayyar manufa su jefa kasar ciki bala’i da wahalhalun rayuwa ba.