✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar #EndSARS za ta tsallaka Afirka ta Kudu

Daruruwan ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu sun ce za su bi sahun takwarorinsu na Najeriya wajen yin tattakin goyon baya

Daruruwan ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu sun ce za su bi sahun takwarorinsu na Najeriya wajen yin tattakin goyon baya domin neman kawo karshen danniyar jami’an ‘yan sanda da kuma neman ingantuwar shugabanci.

Sun bayyana matsayin nasu ne a wata sanarwa da shugaban Kungiyar ‘Yan Najeriya Mazauna Afirka ta Kudu (NUSA) Mista Adetola Olubajo ya fitar hannu ranar Litinin a Legas.

Sanarwar ta ce, “A ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba 2020, ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu za su yi tattakin lumana zuwa ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Pretoria.

“Za mu aike da wasika zuwa jakadan Najeriya a can, Ambasada Kabir Bala.

“Mun yi ta bin sahun wannan zanga-zangar tun ranar da aka fara ta kuma muna son ganin matakin da gwamnati za ta dauka.

“Amma rashin gamsuwa da yadda gwamnatin take tafiyar da lamarin, ya sa muka ga ya zama wajibi mu bayar da namu tallafin ta hanyar kira ga gwamnatin Najeriya kan ta saurari koke-koken miliyoyin matasan Najeriya a fadin duniya.

“A kan haka ne muke gayyatar kafafen watsa labarai domin su zo su dauki yadda za ta kaya yayin tattakin namu,” inji sanarwar.

Zanga-zangar dai da ta fara a ‘yan kwanakin baya kan neman a rushe sashen rundunar tsaro mai yaki da ‘yan fashi ta SARS na neman daukar sabon salo.

Ko a karshen makon day a gabata dai sai da masu zanga-zangar suka kaiwa gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola hari yayin da a ranar Litinin kuma wasu fusatattun matasa suka fasa gidan yarin birnin Benin na jihar Edo tare da sakin fursunoni.