Da Dumi Dumi

Zanga-zangar Sudan: Shugaban Rikon Sudan ya gana da Shugaban Masar

Janar Muhammad Hamdan Daglo na Sudan
Janar Muhammad Hamdan Daglo na Sudan

Babban Hafsan Sojojin Kasar Sudan kuma Shugaban Gwamnatin Riko Kasar Janar Muhammad Hamdan Daglo, ya kai ziyara kasar Masar domin wata tattaunawa da Shugaban Masar Janar Abdul Fattah Al-sisi bayan zargin da ake yi wa sojijin Sudan din na nuna karfin da ya wuce ka’ida ga fararen hula masu zanga-zanga.

Wannan ne karo na farko da Shugaban mulkin sojin ya kai ziyarar aiki kasar Masar. A wata sanarwa da Mataimakin Hafsan Sojojin Sudan da aka fi sani da Janar Hemet ya ce, “Sun tattauna ci gaban da aka samu a halin da ake ciki dangane da rikicin Sudan.”

Shugaba Al-sisi wanda shi ma tsohon Babban Hafsan Sojin Masar ne kafin daga bisani ya zama Shugaban Kasa ya bayyana irin kudirin da suke da shi a kasar ta Sudan domin taimakawa wajen samun daidaito da kuma samar da zaman lafiya a Sudan da makwabtanta,” inji Fadar Shugaban Masar.

Alkahira da Khartum sun kulla dangantaka mai karfi a tsakaninsu tun bayan da aka yi wa Umar El-Bashir juyin mulki a 11 ga watan Afrilun 2019 bayan shafe watanni ana zanga-zanga a kasar.

Hemeti, ya ce suna neman hadin kan kasashen Larabawa domin samar da zaman lafiya mai dorewa inda a watan Mayun da ya gabata suka gana da Yarima Muhammad bin Salman na Saudiyya domin samun hadin kai.

ADVERTISEMENT

Tarzomar da ta taso cikin watan Satumban bara wacce aka fara ta a kan karin kudin burodi daga bisani ta rikide ta koma ta neman ’yanci daga mulkin Janar Umar  Al-Bashri wanda ya shafe shekara 30 yana mulkar kasar.

Zanga-zangar ta ci gaba bayan hambarar da Shugaban da aka yi, don ganin a koma mulkin dimokuradiyya

A ranar 3 ga Yuni an kashe akalla masu zanga-zanga 127 sannan wadansu da dama suka jikkata, kamar yadda likitocin da suke da alaka da zanga-zangar su shaida.

Wani bayanan masu shigar da kara sun tabbatar da wani hari da rundunar sojin ta kai a kan masu zanga-zanga, cewa sun kai harin ne ba tare da umarni ba.

Hemeti, ya sha musunta zargin da ake yi wa dakarunsa kan kai wannan hari, wanda ya ja hankalin kasashen duniya.

Ganawar dai da Janar Hamdan ya yi da Sisi na Masar ta zo ne bayan da ’yan sanda suka jefa barkonan tsohuwa a kan masu zanga-zanga, inda suka bukaci a gudanar da bincike a kan harin watan Yuni da aka kai kan masu zanga-zanga.

A 17 ga watan Yuli ne dai masu zanga-zangar da sojojin da suke rike da madafun iko suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa a tsakanin sojoji da farar hula, kafin a koma tsarin dimokuradiyya baki daya.

A shekaranjiya Laraba, rahotanni daga kasar sun nuna cewa alkalla mutum 5 sun rasa rayukansu sakamakon bude wuta kan masu zanga-zanga da sojoji suka yi.

 

 

Share