✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zantukan zarar Zaira

A majigin kyautata rayuwa ’Yan lalle na karuwa Adon gari na moruwa Amarsu na dada soyuwa Agogon ango na juyuwa   A a Akwakun Arewatawa…

A majigin kyautata rayuwa

’Yan lalle na karuwa

Adon gari na moruwa

Amarsu na dada soyuwa

Agogon ango na juyuwa

 

A a Akwakun Arewatawa

Ana ganin tariyar Turkawa

Gadar adon-gari mai kayatarwa

Kai-kawon ’yan lalle ba kakkautawa

Tamfar damar karamin laujen Mekzikawa

 

Zakuwar zakakura

Zakalkalewar zankakurin zakara

Zumun zaman Zaira

Zilliyar zarra

Zumudin Zahara

 

Zancen zumuncin ziyara

Zirin azara

Zogin zungura

Zazzagar zabura

Ziryar zungureriyar zabira

 

Majigi

Mata da miji

Suna ta cin naman kaji

’Ya’ya na sa su bugun kirji

Mirgina-mirginar magagi

 

Akwakun Arewatawa

Karamin laujen tsayuwar kafa guda

Soyuwar  zukata tai gargada

Magabta na gada-gada

Sun ga walkiya da tsawa

 

Turka-turkar Turkawa

Tarairayar  ’ya’ya da uwa

Turancin Turawa

Turereniyar tunkudewa

Tarnakin takurawa

 

Kurtun halo alalo

Ya zam akwakun kallo

Fina-finan soyayya salo-salo

Kulelen Kululu kilo-kilo

Zinariyar Zaira ta azazzalo

 

Facakar facala

Fal-fal din fitila

Falo-falo falla-falla

Falle fululun shafuka falala

 

Kisisina

Kishiya ce karshen magana

Kashe wutar wauta a dangana

Karsashin nuna tsana

Karambanin karon bauna

 

Kutungwila

Sai masu hila

Zancen kila-wa-kala

Rashin tabbacin lalala

Sai masoya su hassala

 

Wasan kwaikwayo

Aikin dan koyo

Yai wa Bab oyoyo

Balaguro aka bibiyo

Batutuwa aka liliyo

 

Al’adun mutan Gabashi

Mun dubi Turai a Yammaci

Rashin daukar komai da muhimmanci

Bahaushe mai ban haushi

An biyoka bashi

 

A yunkura tashi

Innuwar hutu kar ai kashi

Kyawawan ta’adu ai tushi

Kowa ya inganta nashi

Ban da kai wa juna naushi

 

A tada kai da matashi

Jariri sai lallashi

Amarya sai da kunshi

Ango yai ta murmushi

Aure sai da toshi

 

A kasafta albashi

Ciyar da iyali ba  fashi

Uwargida ban da fushi

Ai annashuwa da karsashi

Farka ki ce wa miji tashi-tashi

 

In kai zubin adashi

Kwaso mu ci dashishi

A zuba mai da tasshi

Duk mai so a sammashi

Almajiri ya miko kokonshi

 

Wa-ka-ci-ka tashi

Ko mai neman bashi

An ci masa albasa mai lawashi

An tuka tuwon laushi

Gutsuro lomar geffan sashi

 

Takun saka ya kare

Nuku-nuku an karkare

Magabta sun dare

Masalaha ta sa kowa ya dire

Hirar rana zuwa dare

 

Farfar da fure

Furanni farare

Fikar fere-fere

Fankata-fankantan faya-fayan furfure

Fur tashin tsuntsun tsirin tsere

 

Dimbin masu baje na-mujiyarsu a AKWAKUN AREWATAWA NA KARAMIN LAUJE DA TSAYUWA BISA KAFA GUDA, sun saba kallon majigin mirgina-mirginar zamantakewar rayuwar Turkawa, musamman na MALAMA NISA DA KYAUTATA RAYUWA inda aka yi ZANTUTTUKAN ZARRAR ZAIRA, wata jaruma ’yar talakawa da ta samu soyyyar ATTAJIRI DAN ATTAJIRI,wanda ya yi mata toshi, har ya turke ta a matsayin AMARSU TA ANGO.

Wannan majigi na wasan koyi ka koyar ya nusar da Haurobiyawa tsarin zamantakewa da turka-turkar takun sakar Turkawa kafin su zamo ma’aurata. Domin su ma al’ummar Gabashi da na Yammacin duniya sukan yi fama da KISISINAR KISHIYA, kodayake dai sun fi yin karon-batta da FACAKAR FANCAL-FANCAL DIN FACALA.

Hakika shirye-shiryen AKWAKUN AREWATAWA mai wutsil-wutsil din hotuna yana matukar kayatar da Haurobiyawa, musamman masu yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare da sai-in-sa ba, don haka ma tashar akwatin magana mai wulkita hotunan ke yin faskaren ma’anonin kalallame kalaman Indiyawa da Larabawa da na Turkawa, har ma da na masu murguda baki kamar suna cin kilishi, su kanga gilashi su yi ta yaren Ingilishi, don samar da kiraren nunin fahimtar da Haurobiyawa kan al’amuran rayuwa.

Batu na ingarman karfen karafan kwangirin tarago, ba tare da bata lokaci ko jan kafar wulwulawar agogo ba, ina fatan ’yan wasan majigin KANNEN-AUDU da ke shirya fina-finai a Arewacin Haurobiya sun dauki darasi, musamman ma jin cewa sun kai wa Baban-burin-huriyya ziyarar ban girma.

Lallai akwai bukatar  ’yan wasa da jaruman fina-finan KANNEN-AUDU su rika shirya majigin nusar da al’umma yadda za a warware tsilli-tsilli matsalolin da ke ci wa Haurobiyawa tuwo a kwarya, musamman al’amuran da suka shafi ZAMAN-TAKEWA DA SIYASAR YASAR HAURO DA TATTALIN TUTTULE TULUN TARIN DUKIYA.

Ina ganin aiwatar da managartan tsare-tsare a shirye-shiryen wasan majigin KANNEN-AUDU za su inganta harkokin koyon watsattsake da buga wagagen littattafai, tare da nishadantar da al’umma, ta yadda kowa zai samu annashuwa da karsashin baje na-mujiya da zarar batutuwan jarumanmu sun zarta ZANTUKAN ZARRAR ZAIRA, wadda ake ta nuna mana a AKWAKUN AREWATAWA na karamin lauje da tsayuwa bisa kafa guda.