✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaratan matasan ’yan kwallon Najeriya da tauraronsu ya dusashe cikin sauri

Kamar yadda Hausawa ke cewa, idan ana dara a kan fidda uwa. Haka ma a kullum idan ana batun fitar da zaratan matasan ’yan kwallon…

Kamar yadda Hausawa ke cewa, idan ana dara a kan fidda uwa. Haka ma a kullum idan ana batun fitar da zaratan matasan ’yan kwallon kafa a duniya, Najeriya uwa ce daga Afirka, sannan a duniya ma, ba kanwar lasa ba ce.

A duk lokacin da ake fafata gasar cin kofin duniya ’yan kasa da shekara 17 da 20 da Olamfic, har kasashen Brazil da Ajantina suna dar-dar idan aka hada su da Najeriya.

Babban abin misali a nan shi ne, Najeriya ce ta fi kowace kasa lashe Gasar Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 17 wato U-17, inda ta lashe gasar sau biyar a shekarun 1985 da 1993 da 2007 da 2013 da 2015, sannan kuma ta zo na biyu a shekarun 1987 da 2001 da 2009.

Tana gaba da kasar Brazil, wadda ta lashe gasar sau hudu.

Sannan a duk lokacin da aka kammala gasar, ’yan wasan Najeriya na lashe kyaututtuka da dama, kamar Gwarzon dan wasa, da wanda ya fi zura kwallaye da sauransu.

Wannan ne ya sa Aminiya ta tattaro bayanan wasu zaratan ’yan wasan Najeriya, da suka taso kamar za su cinye komai, amma tautaronsu ya dusashe cikin saurim suka bace kamar ba a yi su ba.

Cristantus Macauley

A shekarar 2007 da aka yi Gasar Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 17, zaratan ’yan wasan duniya da duniyar kwallon ke yayi yanzu sun halarci gasar.

Daga cikin wadanda suka halarci gasar akwai Toni Kroos na Real Madrid da Jamus, da Eden Hazard na Real Madrid da Beljiyum da David De Gea na Manchester United da Spain da sauran zaratan ’yan wasa.

Amma duk da zaratan ’yan wasan nan, Macauley ne ya fi zura kwallaye, inda ya samu kyautar takalmin zinare (Golden Boot), sannan kuma ya zo gwarzon dan wasa na biyu, inda ya karbi kyautar kwallon azurfa (Silver Ball).

Yanzu haka duniyar kwallo na yi da Kroos da De Gea da Hazard, inda kusan yanzu suna cikin wadanda ake magana, amma shi Crisantus Macauley yana kungiyar Zob Ahan SC na kasar Iran. Kusan an daina jin duriyarsa.

Crisantus Macauley a tsakiya tare da Toni Kross a dama da Bojan a hagu Hoto: Getty images

Taiye Taiwo

Mikel Obi tare suka taso da Taiye Taiwo, duk da cewa Mikel ya dan tabuka wani abu, shi Taiye yanzu yana labe a Finland a kungiyar RoPS Rovaniemi, shi kuma Mikel yana Turkiyya.

Sun shiga sahun nan duba da cewa tare suka fara haskawa da Gwarzon Dan Wasan Duniya na yanzu, kuma wanda ya fi kowa samu kyautar, wato Messi da Fagregas da Aguero da sauransu,.

An fara saninsu ne a Gasar Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 20 wanda aka buga a shekarar 2005 a kasar Holland, wadda Ajantina ta lallasa Najeriya da ci 2 babu a wasan karshe.

Bayan wannan kuma, Ajantina ta sake doke Najeriya a Gasar Olymfic.

Tun wannan lokacin, Messi kara gaba yake yi, su kuma ’yan Najeriyas suna kwan-gaba-kwan-baya, duk da cewa za a iya cewa gara Mikel Obi, domin ya dade a Chelsea, inda har Kofin Zakarun Turai ya lashe.

Taiye Taiwo a hagu sai Messi a tsakiya da Mikel a dama Hoto: Getty images

Sani Emmanuel

A Gasar Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 17 ta shekarar 2009 da aka buga a Najeriya, kasar Switzerland ce ta doke Najeriya a wasan karshe.

A gasar, Sani Emmanuel ne ya lashe Takalmin Zinare, na wanda ya fi taka leda wato (Golden Boot).

A gasar akwai zaratan ’yan wasa irinsu Neymar Jnr da Isco da Morata da Coutinho da Casemiro sauransu.

A bara ne aka samu rahoton Sani Emmanuel da ya dade yana kana ba tare da kulob ba yana fama da jinya, amma rashin kudi ya hana a masa tiyata.

Daga baya ne dan wasan Najeriya, Ogenyi Onazi ya dauki aikin, inda ya biya Naira miliyan 1.4.

Abin mamaki, wanda a gasar aka ce ya fi Neymar da Isco taka leda, amma yanzu ba shi da kulob, kuma sai da aka taimaka masa da Naira miliyan 1 da dubu 400 domin jinya.

Sani Emmanuel rike da kyaututtuka biyu Hoto: Getty Images

Sauran wadanda tauraronsu ya dusashe cikin sauri akwai Kelechi Iheanacho wanda yake kungiyar Leicester City, duk da cewa yanzu ya dan fara dawowa da tashe, da Musa Yahaya da FC Porto B, da Abdul Ajagun da Rabiu Ibrahim da Lukman Haruna da Dele Ajiboye da Alampasu da sauransu da dama da suka taso da karfinsu, amma ko dai aka daina jin duriyarsu, ko kuma suke wasa a kananan kungiyoyi.

Kelechi Iheanacho rike da kyaututtuka biyu Hoto: fifa.com