✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin almundahana: EFCC ta sake gurfanar da  Jang a gaban kotu

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati  (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata Jonah Dabid Jang  da tsohon kashiya a…

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati  (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata Jonah Dabid Jang  da tsohon kashiya a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Mista Yusuf Pam a gaban kotu kan zargin almundahanar kudaden Jihar.

Hukumar EFCC ta gurfanar da su ne a  gaban Mai shari’a C.L Dabup na Babban Kotun Jihar  Filato, kan zarge-zarge 17.

An fara wannan shari’a  ce a gaban Mai shari’a Longji wanda kafin ya yi ritaya daga alkalanci  a ranar  31 ga Disamban bara, ya ce wadanda ake zargin suna da tambayoyin da za su amsa kan zarge-zargen da ake yi musu.

Daya daga cikin tuhumar da ake yi wa tsohon Gwamnan ta ce a lokacin da yake Gwamnan Jihar shi da Mista Yusuf Pam, daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2015, sun yi almundahanar Naira biliyan 4 da miliyan 357 da dubu 195, mallakar jihar, wanda hakan ya saba wa tsarin mulkin Najeriya, sashi na 309.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake karar E.G Phajok, (SAN) da S.G Ode sun bukaci a bayar da belin wadanda suke karewa, inda suka roki kotun ta tsaya kan belin da Alkali Longji ya bayar a can baya.

A karshe Mai shari’a Dabup ta bayar da beli ga wadanda ake zargin, inda ta dora kan hujjojin alkali Longji, kuma ta bukaci masu tsaya musu su cika takardu, idan suna so su ci gaba da tsaya musu.

Mai shari’ar ta bayar da kwana uku, domin cika sharuddan belin, kuma ta sanya ranar 28  zuwa 28 ga Mayu  mai zuwa don fara sauraron shari’ar.