Search
Subscribe
Zargin cin hanci: FIFA ta dage Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Ghana har tsawon rayuwarsa

Kwesi Nyantakyi

Zargin cin hanci: FIFA ta dage Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Ghana har tsawon rayuwarsa

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta bayar da sanarwar dage shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana Kwesi Nyantakyi har tsawon rayuwarsa.

Shugaban, wanda ya yi murabus daga rike mukaminsa tun a watan Yunin da ya gabata saboda zargin da ake masa na karbar cin hancin Dala dubu 65 kwatankwacin Naira Miliyan 23 da dubu 400 a wani faifan bidiyo da wani dan jarida dan asalin Ghana Anas Armeyau Anas ya watsa a yanar gizo.  A faifan an nuna yadda tsohon shugaban hukumar yake karbar cin hanci daga wajen wani da ba a tantance ba, da hakan ya janyo ka-ce-na-ce a ciki da wajen Ghana.

Jim kadan bayan  dan jaridar ya watsa faifan bidiyon a yanar gizo ne sai Hukumar FIFA ta kafa kwamitin bincike, inda ta samu tsohon shugaban hukumar da laifi.

Sai dai a yayin da Hukumar ta kafa kwamitin bincike ta umarce shi da ya ajiye mukaminsa sannan ta ci shi tarar Fam dubu 390 kwatankwacin Naira Miliyan 180.

A ranar Talatar da ta wuce ne sai FIFA ta sanar da dage tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana daga shiga harkokin wasanni a ciki da wajen Ghana har tsawon rayuwarsa saboda abin kunyar da ya yi na karbar cin hancin Dala dubu 65.

A nasa bangaren shugaban ya nuna sharri aka yi masa, inda ya ce wata manakisa ce kawai aka shirya masa a faifan bidiyon don a bata masa suna.

Baya ga mukamin da yake rike da shi na shugaban Hukumar kwallon kafa ta Ghana, shi ne mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) kuma  memba ne a Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Yanzu shugaban ya rasa dukkan wadannan mukamai.  Kuma FIFA ta ce tana fata wannan zai zama darasi ga masu karbar cin hanci da rashawa a harkar kwallon kafa.

Idan za a tuna a kwanakin baya ne hukumar ta dage Mataimakin Kocin Najeriya Salisu Yusuf har na tsawon shekara daya saboda zargin da ake masa na karbar cin hanci da rashawa a wani faifan bidiyo da dan jarida mai zaman kansa dan asalin Ghana Anas Armeyaw ya fitar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin