✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin mayar da kowa Musulmi da Bafulatani a Najeriya

Furucin hadama ko kuma na annamimanci da ke cike da cece-kuce da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi a yayin wani taron ibadar Kiristoci…

Furucin hadama ko kuma na annamimanci da ke cike da cece-kuce da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi a yayin wani taron ibadar Kiristoci a Majami’ar Saint Paul da ke Oleh na Karamar Hukumar Isoko ta Kudu cikin Jihar Delta, sam ba su dace da dattijon kasa mai kima irin sa ba. Ya ce: “Yanzu ba a batun cewa wai matsalar Boko Haram ta samo asali ne daga rashin ilmi da kuma rashin aikin yi ga matasanmu a Najeriya, kamar yadda abin ya faro, a’a yanzu abin ya zama batun neman musuluntar da kowa tare da mayar da kowa Bafulatani ala tilas da kuma kitsa aikata miyagun laifukan safarar mutane da fitar da kudade ta haramtacciyar hanya da safarar miyagun kwayoyi da safarar makamai da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da ma kifar da gwamnatoci a  yankin Yammacin Afrika da ma Nahiyar Afrikar gaba daya.”

Sai dai Ministan Watsaa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya mayar wa da Obasanjon martani yana mai cewa, kalaman nasa ba wani abu ba ne illa nufinsa na “kawo farraka” kuma hakan abin a yi Allah wadai ne. Ya kirayi Obasanjon da kada ya kuskura ya bar gabarsa ko hassadar da yake da ita a kan wani ta mamaye soyayyar da yake da ita ga dunkulelliyar Najeriya, yana mai cewa idan Obasanjon ya roki gafarar ‘yan Najeriya a yanzu ya kuma janye miyagun kalaman nasa, to ai bai makara ba. Alhaji Lai Mohammed din ya ci gaba da cewa: “Babban abin damuwa ne matuka, idan har Obasanjon da ya fafata a yakin tabbatar da dunkulalliyar Najeriya kuma ya zamana shi zai yi irin wannan babatun da nufin farraka kasar, a kuma gargarar rayuwarsa a duniya.”

A cewar Ministan, Boko Haram da kuma Kungiyar IS reshen Yammacin Afirka, kungiyoyin ta’addanci ne da rarrabewa tsakanin addinai ko kuma kabila bai cika damun su, a sanda suke aika-aikarsu na kashe-kashe marasa kan gado. Tun fara rikicin Boko Haram, a bayyane yake cewa kungiyar ta fi kashe Musulmi fiye da mabiya sauran addinai tare da ruguza masallatai fiye  da sauran wuraren ibada na wasu addinai na daban kuma ba a san su da ware wadanda danyen aikin nasu ke shafa ba ta fuskar kabila. Don haka, wauta ce karara a ce wai kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP, suna hankoron musuluntar da kowa da kuma mai da kowa Bafulatani a Najeriya ko kuma ma yankin Yammacin Afirkar.

Kai a ma bayyana kalaman na Obasanjo a zaman na neman farraka kasar, ai sassauta kalaman ne kawai aka yi. Sun kai ma a danganta su da ‘kalaman nuna batanci’. Kawai sakamakon kololuwar annamimancinsa, Obasanjon ya kirkiro da kalmar “Yunkurin mayar da kowa Bafulatani” don kawai ya ci mutunci tare da shafa wa kabilun Arewacin Najeriyar kashin kaji a kan matsalolin nan na rashin tsaro da kuma na ‘yan bindiga da yankin ke ciki. Baya ga kisan gillar wasu fitattun ‘yan bokon yankin, kamar su Janar Muhammadu Shuwa, kungiyar ta kuma yi yunkurin kashe Shehun Borno da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da kuma shahararren malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Idan dai har Obasanjo wanda tsohon Shugaban kasa ne na mulkin soja da kuma farar hula, yana da bayanan sirri a kan tsagerun Boko Haram, to dai bai kamata ya yi irin wadannan kalamai a majami’a ba. A matsayinsa na daya daga cikin membobin Majalisar Kasa, da akwai wuraren da ya kamata ya bayar da shawarinsa ga gwamnati, ba tare da ya buge da yin batanci tare da cin mutuncin wani yankin Najeriya ba.

Kusan a daukacin rayuwarsa, Obasanjon ya yi kokari gaya ta fuskar rashin nuna bangaranci na addini ko na kabila, sai dai a yanzu ya so bata rawarsa da tsalle. A baya ana masa kallon dan kishin kasa kuma dattijo, wanda ba a tantama a kan batutuwa na kishin kasa. Kuma hakan ya sa yakan iya caccakar kowace gwamnatin da ba shi ne ya jagoranta ba. Tun shekarar 1979 lokacin da ya bar mulki, Obasanjon ya kasance mai sukar lamirin dukkanin gwamnatocin da suka zo bayansa. Sau tarin yawa yana sukar ne ba tare da hujja ba, sai dai ana ganin kalaman nasa a kan yankin Arewar, sun samo tushe ne daga tsamin dangantakarsa da Shugaba Buhari.

Bai kamata Obasanjo ya yi amfani da tsamin dangantakarsa da Buhari ba wajen neman ruguza hadin kan Najeriya ba. Shawo kan sabaninsa da Buhari ba zai zamana sai ta hanyar gurgunta Najeriya ba. Mutumin da ya yi yaki wajen tabbatar da kasar ta ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya; ya kuma fi kowa dadewa a kan karagar mulki, in an hada mulkinsa na soja da farar hula (shekara 11) bai kamata ya rage darajarsa ba, wajen yin irin wadannan kalamai marasa kai ballantana gindi. Obasanjo ya taba yin kwatankwacin wadannan kalaman a ranar 20 ga watan Janairun bana, inda ya yi yunkurin bata kimar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ya kuma caccaki Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo a kan shirin nan na ‘TraderMoni’, sa’annan ya yi kakkausan suka ga Gwamnatin Buhari a kan gurfanar da tsohon Babban Jojin Najeriya, Mai Shari’ah Walter Onnoghen a gaban kuliya manta sabo, game da tuhumarsa kan rashin bayyana kadarorinsa.

Sanannen abu ne, dukkan kasashen duniyar da suka yi zarra ta fuskar ci gaba, kasashe ne da suka ririta bambance-bambancen da ke tsakininsu yadda ya kamata. Ita ma Gwamnatin Buharin kanta, lallai ne ta daina zarge-zarge marasa kan gado a kan matsalolin tsaron kasa ga jam’iyyun adawa. Irin wadannan zarge-zargen babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a kan dukkan ababuwa da suka tabarbare wa gwamnatin, ba shakka na sanya gwamnatin a gwadabe guda da Cif Obasanjon.