✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zauren majalisun dokoki ya yi tir da yunkurin tsige shugaban majalisar Jihar Ribas

Shugaban zauren shugabannin majalisun dokoki na kasa, wanda shi ne shugaban majalisar dokoki ta Jihar Gombe, Alhaji Inuwa Garba ya yi Allah wadai bisa yadda…

 Alhaji Inuwa Garba, Shugaban zauren shugabannin majalisun dokokiShugaban zauren shugabannin majalisun dokoki na kasa, wanda shi ne shugaban majalisar dokoki ta Jihar Gombe, Alhaji Inuwa Garba ya yi Allah wadai bisa yadda wasu ýan majalisar jihar Ribas 5 cikin 32 suka hada kai da wasu ’yan taádda suka yi yunkurin tsige shugaban majalisar, Mista Otelemaba Dan Amachree.
Alhaji Inuwa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da ’yan jarida a ofishinsa da ke Gombe a karshen mako.
Shugaban ya ce aniyar ýan majalisar ta saba wa sashi na 92, karamin sashi na 2, sakin layi na ‘C’ na kundin tsarin mulkin kasa na shekara ta 1999. “’Yan majalisa na iya tsige shugabansu ne kawai da kuriún kashi biyu cikin uku na jimlarsu”.  Inji shi.
Ya ce zauren shugabannin majalisun dokokin na kasa ya Mista Otelemaba Dan Amachree ya sani a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar ta Ribas, ba Mista Ebans Bibi ba.
A matsayinsa na shugaban zauren, Alhaji Inuwa ya bukaci majalisar dokoki ta tarayya ta dauki mataki a kan wadannan ýan majalisa guda biyar da suka yi yunkurin wannan taáddanci da ya saba wa tsarin mulki don kare ýanci dimokuradiyya.