✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben shugabancin Majalisar Dattawa karo na 9

Ni ba dan lele ba ne – Sanata Ahmed Lawan Ganin cewar Majalisar Dattawa karo ta takwas wa’adinta ya zo karshe a makon nan, Jiga-jigan…

  • Ni ba dan lele ba ne – Sanata Ahmed Lawan

Ganin cewar Majalisar Dattawa karo ta takwas wa’adinta ya zo karshe a makon nan, Jiga-jigan ‘yan takarar neman kujera shugabancin majalisar a karo na tara  sun kara kaimi wajen neman ganin kowannensu ya samu nasarar lashe zaben wannan kujera. Sanata Ahmed Lawan na daya daga cikin wadannan ‘yan takara kuma a tautaunawar da ya yi da wakilanmu ya bayyana manufofinsa da kuma kudurorin da yake da su idan har sauran sanatoci ‘yan uwansa sun amince masa ya zama shugabansu.

 

Ca shi ka fito neman wannan kujera ta shugaban majalisa, ko wane shiri ka yi idan ka samu nasara ga sauran ‘yan majalisa da al’ummar kasa gaba daya?

Wannan takara da na ke yi, na neman zama shugabancin majalisar dattawa na fito ne domin mu yi wa al’ummar kasa aiki, duk irin aiyukan da majalisa yakamata muyi, zamu yi, mu kwantar da hankulanmu, mu hada kai da bada goyon baya da shi shugaban kasa Muhammadu Buhari yake bukata, don yi wa jama’a aikin da suka zabe mu saboda shi, kasan ita wanna kujera ta shugaban majalisar dattawa, ba karamar kujera ba ce,kasan wannan aikin ba, na mutum daya bane, dole ne a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mu ‘yan majalisa da kuma sashin zartarwa, dole ne mu hada kai, da juna kuma kowanne dan majalisa muke bukatar ya kasance yadda zai daba gudumawarsa ba wai kawai ga ‘yan majalisa na APC ba ko na PDP, aiki ne na dukkan ‘yan majalisa, ba  na shugaban majalisa shi kadai ba, ka sani a aikin nan, ana iya samun sabani, to amma idan aka samu hadin kai komai zai so da sauki don yiwa al’ummar kasa aiki. Kuma muna tuntubar sauran ‘yan majalisa da ake sa ran za a rantsar da mu a watan yuni, muna bayyayana musu manufofinmu,domin aikin nan bana mutum daya bane,kamar yadda na fada, don a wani lokaci akan iya samun sabani a tsakanin majalisa da sashin zartarwa kuman tabbas za a samu, to ni na kudiri aniyar tabbatar da cewar wannan sabani bai kawo cikas ba, wajen aiwatar da ayyukan  majalisa, domin mu dai an zabe mu don mu yiwa al’umma aiki,haka su ma sashin zartarwa an zabe su don yi wa al’umma aiki, don haka b azan taba bari wai sabani ko rashin fahimtar juna ta kawo tsaiko ga ayyukan ci gaban al’ummar kasa ba. Fatan mu shi ne Allah yayi mana jagora ga wadannan kudurori namu,kuma ‘yan Najeriya sun rinka yi mana adu’a,wajen ganin mun aiwatar da wannan nauyi, zan rike amanar shugaban kasa da al’ummarta da kuma jami’yar mu ta APC domin ci gaban kasar nan.

Sanata, maganar harkar tsaro yaya za ka yi don magance wannan matsala ta rashin tsaro, mussaman a shiyyar da ka fito ta Arewa Maso Gabas.

Lamarin tsaro abu da yake da muhimmaci ga ci gaban kowacce kasa,domin idan ka tuna a kafin zuwan wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ‘yan Boko Haram suna ci karensu babu babbaka, sun kwace garuruwa da dama, har ta kai suna da shalkwatarsu a garin Mubi na jihar Adamawa,kasan tuna baya shi ne roko, babu abin da zamu ce, mu al’umomin jihohin Borno, Yobe da Adamawa sai mu godewa Allah domin shugaban kasa a wancan lokaci, umartar manyan hafsan jami’an tsaron kasar nan, yayi akan su koma hedikwatocin zuwa shiyyar arewa maso gabas, yanzu babu Boko Haram sai dai dan abin da ba za a rasa ba. A shirye nake Insha Allahu idan an rantsar damu, kuma ‘yan majalisa sun bani dama in zama shugaban majalisar,za mu hada kai da sashin zartarwa don ganin an inganta harkar tsaro a fadin kasar nan, sai dai kuma an samu koma baya wanda zamu ce sabon abu ne, matsalar garkuwa da mutane da ta ‘yan bindiga dadi da, a yanzu suka addabi al’ummar sashin arewa maso yamma abin takaici ne, kuma duk abin da ya samu wani sashi na kasar nan, ya shafi kasar nan gaba daya,tun da yayin da sashin arewa maso gabas yake fama da rikicin Boko Haram sauran sassan kasar nan basu samu nutsuwa ba, don haka wannan matsala ta masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga dadi,abar a dauki kwararan matakan dakile lamarin, fatan mu shi ne gwamnati ta gano bakin zaren magance matsalar, a kubutar da kasar nan daga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, ta kowacce hanya,hanyar bi tayin amfani da karfi da bindiga,ita ma hanya ce, amma watakila hanya ta farfado da tattalin arzikin kasa a samawa matasa ayyukan yi, ba wai aikin gwamnati ba, shi ma zai taimaka wajen magance matsalar, Insha Allahu idan ya bamu dama an rantsar damu zamu aiki da gwamnati domin shawo kan lamarin.

Wasu suna ganin kai dan lele ne a Jam’iyyar APC, domin alamu na nuni kana sahun gaba, wanda jam’iyar take mara wa baya, don ganin ka hau wannan kujera ta shugabancin Majalisar Dattawa.

To dai ban cika son in yi magana akan ko ni dan lele ba ne,amma tun da ka tambaye ni, dole in ce,wani abu,na farko dai ni, ba dan lele ba ne, ni dan jam’iyar APC ne mai biyayya, mai akidar ci gaba, sabo da tarihin siyasa ta tun da na fara siyasa kullum ina cikin jam’iya mai son,mai son ci gaban al’umma,kama tun da UNCP har zuwa APC.Kai asali ma ni,dan NEPU ne, domin iyayena ita suka yi. Yadda aka tafiyar da al’amura a baya na jefa mutane cikin halin talauci da kwashe dukiyar kasa wadda waccen Gwamnati tayi, da wasu shafaffu da mai suka rinka yiwa tattalin arzikin kasar nan wa kaci ka tashi, hakika,al’umma ba zata taba zama lafiya ba, muddim jama’a suna cikin halin talauci, dan abin da wannan gwamnati tazo ta samu wanda bai taka kara ya karya ba,ta toshe hanyoyin yin sata da wawure kudaden al’umma,yau irin wannan halin da muke ciki ya zama dole ayi maganin duk wani barawo, to da wannan akida ni nake kai, da kuma jam’yar APC, idan har jam’iya ta bani kafa dole ne in yi biyyaya,kuma don jam’iya ta nuna ni take son in zama dan takara, ba fa wai in zama shugaban majalisa dattawa ba,tun da kaga dan takara ne, ai sai na zabe ne, watakila ganin irin kware wa ta da shekarun dana shafe a majalisa kusan 20 da kuma mukamin da nake rike da shi, shi ne dalilan da yasa jam’iyar ta nuna ni.don haka ni ba dan lele ba ne, Su kansu ‘yan uwana, ‘yan majalisa sun je wajen shugaban jam’iya Adam Oshoimole da sauran manyan shugabannin jam’iya suka nuna son goyon bayansu gare ni.iyaka dai mun san Allah ne mai bayar da mulkin,kuma idan Allah ya bani wannan nauyi mu sani amana ce ta mutane,don haka hakki ne babba, mu rike amanar jam’iyar da al’umma kasa baki daya da dukkan yan majalisar da suka zabemu zuwa wannan matsayi.

Jama’a suna ganin tun da jam’iyarka APC ta nuna goyon bayanta gare ka ba kuwa za ka zama dan amshin Shata ba, sai abin da suke bukata za ka yi.

Dan amshin Shata yaya yake? To ka gaya min abin da Shugaban Kasa, yake so wanda ba ya da kyau, meye ne wanda shugaban kasar nan, yake so,talakawa basa so,ko kai baka so, shugaban kasa yana son a inganta tsaro a magance ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran ‘yan ta’adda, yana son a daina sace dukiyar kasa,da kuma yaki da cin hanci da rashawa,ka gaya min wannane daga cikin wadannan talakawa basa so,saboda haka idan ya kawo kudiri don ci gaban kasa ko neman kudi da za a bunkasa tsaro, shi ke nan sai ace ba zamu yi ba, saboda idan mu bashi za a ce mu zama ‘yan amshin shata, to za mu ba shi mun kuma mu zama ‘yan amshin Shatan.

Sanata akwai matsalar da ke ci wa mutane tuwo a kwarya na yawan kudaden da ‘yan majalisa suke karba, kuma talakawa na ganin wannan majalisa ta 8 ta yi wa Shugaba Buhari zagon kasa, wajen aiwatar da ayyukansa, wanne abu za ka yi don kauce wa fadawa irin wancan hali idan ka zama shugaban Majalisar Dattawa?

Na farko dai in an ce kudi ake ba ‘yan majalisa, magana ce a rufe a dunkule, ya kamata a bayyana wa mutane wadanne irin kudade ake bayarwa. Yayin da duk ka aiki mutum ko ka ba shi aiki ya kamata ka ba shi kudin da zai kai shi inda ka aike shi, ko ya aiwatar da wannan aiki don haka idan ka ce ‘yan majalisa ne za su yi dokokin da suka shafi rayuwar kowa a kasar nan, duk abin da za a yi majalisa na da dama tayi doka a kai, don haka dole ne, wadanda za su yi dokoki a ba su kayan aiki, da za su yi aikin nan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da ilimi, don haka masu yin dokoki dole ne a basu kudi,don gudanar da wannan aiki,domin haka babu laifi idan har ka sa mutum aiki ka bashi kudin babu laifi, amma dai mu ‘yan majalisa hakki ne a wuyan mu, mu rike amanar al’ummar kasa.

Ka yi zawarcin sauran Sanatoci, yaya ko haka ta cin ma ruwa kuwa?

Ba zawarci na yi ba, illa godiya muka je yi, bisa irin goyon bayan da gwamnonin suka bamu, domin jawo hankalin sanatocinsu a kan amince min, na zama shugaban Majalisar Dattawan, kuma ba wai kawai gwamnonin jam’iyar APC ba har na PDP sun bamu goyon bayansu,domin cimma nasara, Godiya muke ga dukkan al’umma wannan babban aiki ne,domin hannu daya baya daukar jinka, don haka dole ne mu hada kai domin samun nasara.