✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zawarcin APC ga Obasanjo: Girma ya fadi

A lokacin da na ga fuskar Janar Buhari kusa da Obasanjo a cikin hoton jiga-jigan jam’iyyar adawa ta APC da jaridun makon jiya suka buga…

A lokacin da na ga fuskar Janar Buhari kusa da Obasanjo a cikin hoton jiga-jigan jam’iyyar adawa ta APC da jaridun makon jiya suka buga a fuskokinsu, abin ya ba ni matukar mamaki. Na shiga jimami tare da tambayar kaina cewa, shin anya kuwa Buhari ne nan cikin tawagar masu zawarcin Obasanjo? Shin Janar din nan ne da na sani mai tsattsauran ra’ayi, mai akidar adawar innanaha da almundahana yake tsaye cikin fara’a kusa da mutumin da ya haddasa mana jamhuru a kasar nan?
Masu iya magana sun ce, yaro bari murna karenka ya kama zaki. Domin kuwa wasunmu da suka rika doki da murnar cewa an samu kakkarfar jam’iyyar adawa, sai ga shi ba a je ko’ina ba mun ga bambarakwai, mun gane abin ashe holoko ne; hadarin kaka. Idan ba haka ba, yaushe za a ce kungiyar ’yan siyasa masu hankali, wadanda suka san abin da suke yi za su ma yi tunanin zawarcin mutumin da shi ne haddasunar rikita siyasar Najeriya, kawai saboda suna tunanin yana da wata gudunmowa da zai bayar? Babu ma abin takaicin da ya kai irin rainin wayon da Cif Obasanjo ya nuna wa maziyartan nasa, inda ya yi musu tilawa game da siyasa.
Ku ji abin da yake fada: “Ni dan dimokuradiyya ne kuma daya daga cikin shika-shikan dimokuradiyya, ita ce adawa… Babu shakka na yi amanna da cewa irin siyasar da kuke gudanarwa, siyasa ce ta lumana, ba siyasar gaba ba. Kuna gudanar da ita cikin tsafta tare da kishin Najeriya a zukatanku.”
Mu kuwa ai an sha mu mun warke, domin kuwa muna sane da irin bakar siyasar da Obasanjo ya gudanar a kasar nan a lokacin mulkinsa. Mun san irin yadda ya yi gaba da ’yan adawa, kamar kuma yadda ya gasa musu aya a hannu. Haka a cikin jam’iyyarsa, sai da ya uzura wa masu adawa da salon mulkinsa na shekara takwas da ya gudanar a Najeriya. A takaice, shi bai cancanta a ce ma ya yi magana ba, idan dai ana batun yadda ya kamata a yi wa ’yan adawa adalci. Idan na kalli batunsa na cewa, ana siyasar kishin Najeriya a zuciya, nakan tuno da batunsa da yake cewa: ‘Idan babu tazarce, ba Najeriya,’ kamar yadda El-rufa’i ya ruwaito a littafinsa.
Hakika, jawabin Obasanjo abin takaici ne. Kodayake su da suka ziyarce shi, sun samu wando daidai kugunsu! Irin tsallen badake da dokin da ya ja musu har suka ga cewa ya dace su gayyato wannan gayyar-na-gayyaron (tsohon Shugaban kasa) ruwansu ne, ba ruwan kowa ba, musamman ma idan abin ya kwabe. A makonni biyu da suka gabata, ni ban ga dalilin da ya sanya mutane a kasar nan suka shiga doki da zakwadi ba, kawai don Obasanjo ya rubuta wa Jonathan wasikar tonon-silili. Ta yaya ma za a yi a ce wannan mutumin, wanda shi ne ya yi kutu-kutun jefa mu cikin wannan matsalar mulki da muke ciki, sannan kuma zai zagayo ya ce muna da matsala?
Ni dai kam a gaskiya ban ma bata lokacina na karanta wasikar ba, domin kuwa ba ni da lokacin da zan karanta ballagazan munafunci. Amma duk da haka, na karanta rahotannin da jaridu suka rubuta game da wasikar. Ni a ganina, tuni ya kamata a ce mutumin nan yana garkame a gidan jarun, musamman idan muka yi la’akari da muguwar barnar da aka tafka a karkashin mulkinsa na shekara takwas. Amma dai abin takaici ne, wanda kuma ba za mu amince da shi ba, idan ya ce zai nuna shi wankakke ne, har ya ce zai rubuta wasikar kyarar wani.
Shin ko Obasanjo ya mance da sauri, yadda ya yi ta hakilon ganin cewa sai Jonathan ya ci gaba da mulki a 2011? Yana zaton za mu iya mancewa da sauri, yadda shi kadai ya kashe tsarin karba-karba, don kada wani ya amshi mulki daga hannun Jonathan? Yanzu ne zai zo ya ce mana dan nasa da ya goya a 2011 bai cancanta ba?
Ni dai na kadu da mamaki a lokacn da na ga wasu mutane har suna da karfin gwiwar yaba wa wasikar Obasanjo, kawai don wasu sassanta sun fadi gaskiya game da mulkin Jonathan. Shin mutanen da ke yabawa da wasikar, ko suna zaton cewa Obasanjo zai iya rubuta ta, idan a ce ba su babe da dan goyon nasa ba? Duk abin da ya rubuta a wasikarsa, ya amayar da bakin cikin da ke tattare da shi ne, domin ya ga dan da ya goya ya kore shi daga gidan da ya gina. Da har yanzu Jonathan yana ladabi ga Baba, yana amsar umurni daga Otta, da ba za ka ji komai daga bakinsa ba, balle ma ya rubuta wata wasikar terere. Ita kanta wasikar amsa da Jonahan ya mayar wa Obasanjo, ban bata lokacina na karanta ta ba, domin kuwa na gwammace in yi amfani da mintuna 30 wajen hada wa iyalina abinci.
Yanzu dai tun da wadannan hamshakan mutane sun zubar da girmansu sun kai wa Obasanjo ziyara, ya ga fuskokinsu. Mu kuma sai mu fara neman hakikanin ’yan adawa, wadanda za su yi wa al’umma yaki na gaskiya a siyasar Najeriya, domin kuwa wadannan dai sun kasa. Lallai babban rimi ya fadi, inda gauraki ke kwana!