✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zidane na son Sadio Mane a Real Madrid

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya fara farautar dan wasan Senegal Sadio Mane na kungiyar Liberpool. Kafar labarai ta France Football ta ruwaito cewa Sadio…

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya fara farautar dan wasan Senegal Sadio Mane na kungiyar Liberpool.

Kafar labarai ta France Football ta ruwaito cewa Sadio Mane ya kasance dan wasa na farko da Zidane ya fara nuna sha’awar yana son kawowa  Real Madrid.

Zidane da ke neman wanda zai maye gurbin Ronaldo, rahotanni sun ce yana yana son kawo dan wasan na Senegal ne a lokacin bazara, wato lokacin da aka bude kasuwar sayar da ’yan wasa.

Chelsea ta yi watsi da tayin da Real Madrid ta yi wa dan wasan Belgium Eden Hazard, mai shekara 28, kamar yadda BBC ta ruwaito daga Daily Record.

Zidane na son kawo Mane ne idan Chelsea ta ki sayar da Hazard duk da cewa ya ki sabunta kwantiraginsa da kulub din na Ingila.

Ana ganin Chelsea za ta zuba manyan kudade a kan Hazard idan har Real Madrid ta dage kan sayen dan wasan.