✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zidane zai sallami golan Madrid Thibaut Courtois

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke Sifen, Zinedine Zidane, ya ce shirye-shirye sun yi nisa wajen sallamar golansa Thibaut Courtois a karshen…

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke Sifen, Zinedine Zidane, ya ce shirye-shirye sun yi nisa wajen sallamar golansa Thibaut Courtois a karshen kakar wasa ta bana.

Kocin ya ce ya gwammace ya yi amfani da Keylor Nabas maimakon Courtois a kakar wasa mai zuwa.

Kulob din Madrid ya sayo Courtois ne daga Chelsea na Ingila a kan Fam miliyan 35 a bara amma zuwa hada wannan rahoto, an zura wa golan kwallaye 42 a raga a wasanni 32 da hakan ya nuna bai yi kokari ba. Hakan ya sa Zidane yake shakku game da kwarewarsa.

Bayan Madrid ta sayo Courtois daga Chelsea sai Keylor Nabas ya koma matsayi na biyu, amma yanzu Zidane yana kokarin mayar da Nabas matsayi na farko da zarar ya sallami Courtois.