✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyara ga zuriyar wadanda suka fi tsayi a Kudancin Kaduna

A jikin dutsen Kagoro da ke Karamar Hukumar Kaura da ke Kudancin Jihar Kaduna akwai wani dogon kabari mai tsawon mita 30 da ake danganta shi…

A jikin dutsen Kagoro da ke Karamar Hukumar Kaura da ke Kudancin Jihar Kaduna akwai wani dogon kabari mai tsawon mita 30 da ake danganta shi da mutumin da ya fi kowa tsayi a Kudancin Kaduna mai Katagwan. Katagwan, wanda tarihi ya nuna ya rayu a yankin tsawon shekara 300 da suka wuce, an mayar da kabarinsa wurin yawon bude-ido, inda yake karbar bakuncin mutane da dama daga ciki da wajen Najeriya.

Ba kawai tsayinsa ne ya fi bayar da mamaki ba, hatta wasu abubuwa da aka ce yana gudanarwa a zamaninsa sun zamo abin kasa kunne a saurara. Ana danganta wasu sawaye da ke saman dutsen gare shi da kuma na karensa da suka rayu a wajen.

An ce saboda tsayinsa a duk lokacin da wani ya yi tu’annuti a yankin ba tare da an gane wa ya aikata ba yakan mika hannunsa mai tsawo ya dauko mutum daga gidansa. Sannan saboda tsayinsa yakan hango abokan gaba idan ana shirin kawo musu hari daga nesa. “Kuma daga nan wurin idan yana zaune yakan hango duk abin da ke faruwa a yankin Kafanchan,” inji Suwanta Zako, daya daga cikin zuriyar Katagwan a tattaunawa da Aminiya.

An ce a lokacin da zai bar duniya shi da kansa ya tona inda za a binne shi a dutsen Kagoro kuma da ranar ta zo ya je ya kwanta a cikin ramin bayan ya umarci ’ya’yansa da sauran makwabta su binne shi idan ya rasu. Har yanzu kabarinsa mai tsawon mita 30 na nan inda Gwamnatin Jihar Kaduna ta mayar da wajen wurin yawon bude ido a Dutsen Kagoro, kamar yadda wakilin Aminiya ya je ya gano tare da daya daga cikin zuriyarsa.

Daga cikin zuriyar Katagwan ne aka yi mutumin da ya fi kowa tsayi a wannan zamani a yankin, wanda ake ganin ba kawai a Kudancin jihar ba, hatta a Jihar Kaduna samun wanda ya kere shi a tsawo sai an laluba.

Dan kimanin shekara 26, Ezra Suwanta Zako, mai tsawon kafa 7, shi ne mutumin da ake tsammanin ya fi kowa tsawo a fadin Jihar Kaduna, a kididdigar da ba ta hukuma ba.

Da Aminiya ta je garin Dusai da ke hanyar Kagoro zuwa Manchok a Karamar Hukumar Kaura, ta  zanta da shi a cikin wani budadden gida mai dakuna hudu.

Ezra, wanda aka fi sani da Dogo, ya shaida wa Aminiya cewa ya taso ne kamar yadda kowane yaro ke tasowa a yankin, inda ya fara karatunsa na firamare, sai dai burinsa na kammala karatu bai cika ba domin kamar yadda ya shaida wa Aminiya, karatunsa ya tsaya cak a yayin da ya kai matakin aji biyar a babban sakandaren gwamnati sanadiyyar rashin kudin ci gaba da karatu kuma babu mai ci gaba da tallafa masa.

Ya ce da farko yana nuna damuwa idan yara na tsokanarsa kan tsawonsa, amma daga baya ya fi kowa alfahari da irin tsawon da yake da shi. “Ban ga dalilin ci gaba da damuwa ba bayan na san haka Allah Ya so ya yi ni,” inji shi.

Game da yadda yake ji, Dogo ya ce yana daukar kansa kamar kowa ne, sai dai yakan motsa jikinsa ta hanyar doguwar tafiya da kafa da kuma wasan kwallon kwando wanda har Kaduna ya taba zuwa a sanadiyyar wasa.

Ya ce babu wani kalubale da yake fuskanta da ya wuce irin wanda kowa ke iya fuskanta a rayuwa. “Na taba yin aiki da Kamfanin Coca Cola da ke Suleja a Jihar Neja inda daga baya na bari da kaina saboda matsalolin da nake fuskanta a wajen.

“Haka na hakura na dawo gida na ci gaba da sana’ata ta sakar matankadi da yin noma da kuma leburancin gine-gine. Bayan nan kuma ina sha’awar tukin babbar mota,” Inji shi. Kan yanayin yadda zirga-zirgarsa ke kasancewa, Dogo ya ce ya fi sha’awar hawa babur sai dai ya ce ba ya fuskantar matsala wajen shiga babbar mota ko budaddiya. Amma yayin hawa karamar mota sai an ja kujerar zamansa zuwa baya daga gidan gaba kafin ya ke iya zama ta yadda a wani lokaci ma sai ya fito da kansa ta waje yake jin dadin zama.

“Amma dangane da kayan sawa ina da tela na musamman da ke gwada ni shi ya san komai na fadi da tsawona. Takalma kuwa a kan hada min nawa ne musamman,” inji shi.

Game da aure kuwa, Dogo ya ce yana san ran gaba kadan zai samu abokiyar zama domin a cewarsa, mata na rububi a kansa. “Burin kowace mace shi ne a ce Dogo ne saurayinta. Haka za ka ga suna ta rububin yin hotuna da ni,” inji shi.

Suwanta Zako, mai kimanin shekara 80, shi ne mahaifin Ezra kuma ya shaida wa Aminiya cewa yana alfahari da tsayin dan nasa, saboda tunawa da tsatson da suka fito na Katagwan, abin alfaharinsu.

“Shi ne na hudu daga cikin ’ya’ya biyar da suka rage min cikin ’ya’ya 10 da na haifa kuma shi kadai ne ya gaji wannan tsawo,” inji shi.

A karshe mahaifin ya yi kira ga ’yan siyasa da gwamnati su taimaka wa dan nasa da jari ko wani aiki don tallafa masa kasancewar ko karatun sakandare bai kammala ba, kuma ga shi suna cikin halin talauci da suke bukatar taimako. A cikin kundin tarihin abubuwa na musamman, Guiness Book, an bayyana Robert Wadlow a matsayim wanda ya fi kowa tsayi a duniya bayan gwajin da aka yi masa a ranar 27 ga Yunin 1940 inda aka same shi da tsawon kafa takwas da inchi 11 da digo  1, yayin da Azeez Oladimeji daga Jihar Lagos ake zaton shi ya fi kowa tsayi a Najeriya (amma ba a hukumance ba), bayan gwajin da aka yi masa inda aka same shi da tsayin kafa bakwai da inchi hudu, sai shi wannan na Kudancin Kaduna mai tsawon kafa bakwai ba inchi daya.