✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar Buhari a Maiduguri ta bar baya da kura

  Akwai gazawar sarakuna da shugabannin al’umma – Buhari   ‘Ba mu ji dadin rashin zuwan Shugaban Auno ba’ A makon da ya gabata ne…

  •   Akwai gazawar sarakuna da shugabannin al’umma – Buhari
  •   ‘Ba mu ji dadin rashin zuwan Shugaban Auno ba’

A makon da ya gabata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa Maiduguri kan hallaka rayukan mutum 30 da ake zargin ’yan Boko Haram da yi a garin Auno a ranar 9 ga Fabrairu 2020.

Shugaban wanda ya isa Maiduguri da karfe 12:45 ya samu tarbar Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, inda suka yi wata ganawa ta sirri kafin Shugaban da mai masaukinsa suka zarce zuwa Fadar Shehun Borno, inda a nan Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga Shehun Borno kan rasuwar ’yarsa Ya Maira da nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya faru a garin Auno, inda Shugaban ya bayyana bakin cikinsa.

Shugaba Buhari ya cew ya zo Maiduguri ne domin abu biyu, na farko ya yi wa jama’ar Jihar Borno ta’aziyyar mutanen da aka kashe, sannan ya mika ta’aziyyarsa ga Shehun, sai ya nanata aniyar gwamnatinsa ta kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. Ya ce Rundunar Sojin Najeriya za ta kara kaimi tare da wani sabon salo, ita da sauran hukumomin tsaro da hadin kan sarakuna da jama’ar gari wajen yaki da matsalar tsaro.

Ya ce akwai bukatar hadin kan sarakunan gargajiya wajen yakin da Boko Haram, inda ya ce babu yadda za a yi ’yan Boko Haram su kawo hari har cikin Maiduguri ba tare da sanin shugabannin garin ba.

Buhari ya sake ba jama’a tabbacin cewa zai yi duk abin da ya kamata, domin ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a kasar nan, inda ya ce a lokacin yakin neman zabensa ya tabo batutuwa muhimmai uku, harkar tsaro, bunkasa tattalin arzikin da kuma yaki da cin hanci da rashawa, “Kuma muna kokarin a dukkan fannonin,” inji Buhari.

A jawabin Shehun Borno, ya gode wa Shugaba Buhari kan ziyarar da ya kawo, ya ce hakika hakan ya nuna irin kaunar da Shugaban yake da ita ga al’ummar Jihar Borno. Ya roki Shugaban Kasar kan a kara daukar matakai na mussaman kan harkar tsaro a kasar nan.

A jawabin Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yabawa ya yi da wannan ziyara ta Shugaba Buhari, inda ya yi kira ga hukumomin tsaro su kara zage damtse a yakin da ake da Boko Haram.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da wadansu mutane kan ziyarar ta Shugaba Buhari, Malam Nadabo Zakin Nama cewa ya yi abin a yaba ne, “Sai dai ya kamata a ce Shugaban ya ziyarci garin Auno, inda aka hallaka bayin Allah babu gaira babu dalili, saboda sakacin jami’an tsaronmu,” inji shi, inda ya yi kira ga Shugaban Kasar ya sa a daina hana motoci shigowa gari, alhali dare bai yi ba.

Shi kuwa Kabiru Mai Agogo cewa ya yi wannan ziyara ba ta da wani amfani tunda bai je garin Auno ba, “Mu jama’ar Jihar Borno ba mu da wani abu da za mu ci gaba da yi, illa addu’ar Allah Ya kawo mana karshen wannan lamari,” inji shi.

Ziyarar ta Shugaba Buhari ta samu ’yan tangarda inda wadansu suka rika yi wa ayarinsa ihu cewa “Ba ma so!”

Jim kadan bayan tafiyar Shugaban, wadanda ake zargin ’yan Boko Haram sun kai hari garin Maiduguri ta Unguwar Polo, inda aka yi ta jin karar harbe-harben bindiga.

A ranar Lahadin da ta gabata ce ’yan Boko Haram suka kai mummunan hari a garin Auno, inda suka kash mutum 30, ciki har da wadanda suka kone kurmus.

An kai harin ne da misalin karfe 9:50 na dare bayan an rufe hanya, wanda ya tursasa matafiyan suka kwana a wajen.

Wani direba mai suna Ibrahim da Aminiya ta tattauna da shi ya bayyana yadda ya tsere da yadda ya tarar da gawarwakin mutanen. Ya ce ya isa garin Auno daga Damaturu da msalin karfe 4: 45 amma aka ce an rufe hanya. Ya ce da misalin karfe 9:45 na dare, wadanda ake zargi ’yan Boko Haram ne suka shigo musu cikin farin kaya, suka fara kabara da harbi, inda shi da sauran jama’a Allah Ya ba su sa’a suka gudu cikin daji.

Malam Suleiman Ayuba (Yellow) wanda ya rasa kanwarsa da ’ya’yanta a harin ya ce hakika suna cikin jimamin wannan bala’i da ya auka musu. Sai ya ce a matsayinsu na Musulmi sun yarda da kaddarar Ubangiji, kuma yana addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.

A ziyarar da Gwamna Zulum ya kai garin Auno, ya nuna bacin ransa, kan halin da aka jefa jama’a, sannan ya mika ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasu.