✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar fadar Sarkin Musulmin Nijar

A ranar 13 ga Nuwambar 2013, na samu damar kai ziyara fadar Mai alfarm Sarkin Musulumin Nijar, Sultan na Agadas, Alhaji Omar Ibrahim Omar. Duk…

A ranar 13 ga Nuwambar 2013, na samu damar kai ziyara fadar Mai alfarm Sarkin Musulumin Nijar, Sultan na Agadas, Alhaji Omar Ibrahim Omar. Duk da cewar Mai alfarma bai yi hira da jaridarmu ba, kuma bai ce wa daukacin ’yan Najeriyar da suka ziyarce shi uffan ba, na yi matukar farin ciki, domin ya san mun halarci bikin bianou; kuma mu bakinsa ne. Uwa – uba, an ba mu damar kewaya fadarsa.
Ni da taron daliban Kwalejin Irshadil Umma, mun tafi birnin Agadas, tun a ranar 11 ga Nuwamba, amma ba mu isa ba, har sai ranar 12 ga wata, wannan kuwa ya auku ne saboda matsalar da motarmu ta samu, inda ta rika tafiya da baya-baya, ta ki kuma yin motsi zuwa gaba. Sabod ahaka sai muka kwana a wani kauye da ake kira Silika (kusa da Gidan Mai gari Silika), wato kimanin kilomita 253 daga birnin Agadas. Cikin sa’ar da muka yi, muna tare da wakilin Mai alfarma Sarkin Musulmin Agadas a Najeriya (Hakimin Sarki a Najeriya, Sardaunan abzin, Dokta Abdulkadir Labaran Koguna. Da ya fahimci mawuyacin halin da muka shiga, sai Sardauna ya hau babur da Gimbiya (diyar mai garin Silika) ta taimaka masa da shi (ya zuba musu mai), aka goya shi suka tafi wani wurin da zai iya samun sadarwa ta waya, inda ya buga wayar Gwamnan Gunduma na Aderrbissinat, amma bai dauka ba, don haka muka kwana a cikin Sianna Jeep, kusa da gidan Gimbiyar Silika.
Da sassafe Sardauna ya sake hawa babur suka yi tafiyar kilomita 53 zuwa Aderrbissinat, inda Gwamnan Gunduma ya ba shi mota mai shiga Hamada, wato “Toyota Landcruiser, ta zo ta dauke mu zuwa Agadas, sannan aka biya direban wata babbar mota ta janyo motar da muka tafi da ita zuwa Aderrbissinat.
Da isarmu, cikin dare, sai aka saukemu a wani gidan baki da ake kira Darussala, wanda ba shi da nisa da filin jirgin saman Agadas. Da gari ya waye, sai muka kai ziyara gidajen wadanda muka sba da su a ziyarmu ta farko. Mun ziyarci gidan Sauden Iya (wanda aka fi sani da gidan su Gashura, wato wata budurwa ce da ta shahara a birnin Agadas. Da muka dawo gida za mu kwanta barci, kusan kowa ya shiga dakinsa ya kwanta, sai Sardauna ya zo, ya sanar da mu cewa mun samu izinin ganin Sarkin Musulmi, Sultan na agadas, kuma za mu gana da shi a daidai karfe 8:30 na safe.
Don haka da gari ya waye, sai muka hakura da Karin kumallo, bayan kowa ya shirya, sai muka nufi fada. A kofar fada, mun hadu da dogarai da fadawan sarki a kan dawakai; mun gaisa da su, su ma sun gaishe mu. Ba tare da wani bata lokaci ba, sai suka shigar da mu cikin fada, inda muka samu Sultan a kan doguwar kujera yana jiranmu.
Da muka samu wuri muka zauna akan dardumar tsakar fada, sai Sultan ya daga hannayensa guda biyu, ya yi mana addu’a. Baya ga wannan addu’ar da sarki ya yi wa bakinsa, bai kara cewa komai ba, amma Sardaunan Abzin ya ci gaba da Magana a madadinsa, tamkar dai sarki ne ya ba  shi izini.
Mun yi sa’ar ganin fuskar Sultan, domin bai lullube fuskarsa da rawani ba, tamfar yadda Abzinawa ke yi. Mai alfarma sarkin Musulmin Nijar Mutum ne da alamu suka nuna ya dauki rayuwa da sauki, domin mu kadai ne a cikin fadarsa da Bafade daya, sai kuma sardaunansa da ke yi mana bayani. Wanda duk zai kwatanta maka siffar Sultan, zai gan shi “mutum ne baki da ke sheki, kuma dogo mai cike da kwarjini.”
A lokacin da muka zaku da son jin wasu kalamai daga bakin Sultan, sai Dokta Koguna ya bayyana mana cewa, ‘an ba mu umarni mu kewaya fada mu yi kallo. Kafin mu tashi daga inda muke zaune, sai Sardauna ya fara yi mana jawabi, inda ba mu labarai game da bikin Bianou, wanda ake gudanarwa a kowace shekara har zuwa 10 ga watan Muharram (bisa kidayar watannin musulunci), inda a wannan shekarar aka fara daga ranar 13 ga Nuwamba, a kidayar watannin miladiyya.
Tun daga ranar 17 ga Dhul-hijja Abzinawa ke fara shiri bikin Bianou, wanda a cewar Dokta Abdulkadir Labaran Koguna, ‘an shafe shekara 829 ana gudanar da wannan biki. A lokacin da yake yi wa ’yan Najeriyar da suka ziyarci fada jawabi, ya ce: “Masarautar Agadas ta kasance daular Musulunci, kuma manyan malamai sun fito daga cikin wannan gari, domin gidan Sheikh Jibrila bn Umar, wanda ya koyar da mashahurin malamin nan Sheikh Usman dan Fodiyo yana nan a kusa da gidajen kakanninmu. Dangane da bikin Bianou da ya sa kuka taso daga Najeriya zua Nijar, kimanin shekaru 829 da suka gabata aka yi ana gudanar da shi.”
Da Mai alfarma ya saurari abin da Sardaunansa ya fada, sai muka ga ya girgiza kai, al’amarin da ke nuni da “da yardarsa da amincewarsa’ da abin da wakilinsa na Najeriya ya sanar da bakinsa.
A hakikanin gaskiya, na samu dama wadda ban taba samunta a ko’ina ba, domin ban taba shiga fadar wani Sarki a Najeriya na kewaya ba. Sannan a wani sashe na wannan fadar na ga abubuwan tarihi, domin akwai inda aka sanya hotunan Shugabannin Najeriya da suka gabata; wadannan shugabanni sun hada da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, kuma Firiyimiyan Jihar Arewa da Janar Sani Abacha da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato na mulkin Soja, wato Kanal Yakubu Mu’azu (wanda ya yi mulki a lokacin Sarkin Musulmi Dasuki).
A takaice duk wanda yake son ganin al’ummar da talakawanta da shugabanninsu ke riko da al’ada, sai ya ziyarci birnin Agadas da ke Jamhuriyar Nijar. Domin Bikin bianou da ake gudanarwa a kowace shekara yana nuni da hakikanin al’adun mutanen Abzin, don daukaka masarautarsu da garuruwan da ke karkashinta.