✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar Sanata Yusuf ta jawo mutuwar dan gudun hijira a Taraba

Wani gungun matasa ’yan bangar siyasa sun tayar da hargitsi a karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba a lokacin da Sanata Yusuf A. Yusuf da…

Wani gungun matasa ’yan bangar siyasa sun tayar da hargitsi a karamar Hukumar Bali a Jihar Taraba a lokacin da Sanata Yusuf A. Yusuf da ke wakiltar mazabar Taraba ta Tsakiya ya kai wata ziyarar ganawa da shugabanin jami’yyarsa ta APC da ke karamar hukumar.

Sanata Yusuf ya tafi garin Bali mai nisan kilomita 200 daga Jalingo ne don ganawa da shugabannin APC na karamar hukumar kan niyyarsa ta sake tsayawa takarar sanata a karo na biyu.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa Sanata Yusuf ya isa garin da wata sabuwar mota wacce zai bai wa wanda ya dauka a matsayin daraktan yakin neman zabensa, kuma tuni ’ya’yan jam’iyyar ta APC suna da labarin ziyarar, inda ya sa aka shirya masa gagarumar tarba. Amma a cikin ’ya’yan jam’iyyar akwai wadanda ke adawa da Sanata  Yusuf musamman kan rawar da ya taka wajen kawar da shugabannin jam’iyyar na jihar a karkashin shuganbancin Abdulmumini baki wanda na hannun  damar Maman Taraba ne, wato Ministar Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan.

Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole ya rantsar da Barista Ibrahim El-Sudi a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na  Jihar Taraba inda shi ma ya rantsar da shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 16 da sauran  shugabanninta a jihar.

Wakilinmu ya gano cewa wadanda ke adawa da wannan canji ne  suka haddasa hargitsin, inda da shigar Sanatan da wadanda suka rufa masa baya daga Jalingo da sauran wurare  ofishin Jam’iyyar APC a garin Bali, sai matasan suka soma ihu suna cewa ba ma so! Sannan suka fara jifa da duwatsu.

Majiyarmu ta ce matasan sun fasa gilashin motar Sanatan kirar Jeep, ganin haka ne jami’an tsaron da suke tare da Sanatan suka fara harba barkonon tsohuwa da nufin tarwatsa matasan.

Majiyar ta bayyana wa wakilinmu cewa duk da harba barkonon tsohuwar, matasan ba su daina jefa da duwatsu a kan ayari da ofishin APC wanda sanatan tare da manyan jam’iyyar ke ciki ba.

Ganin lamari zai munana sai wani daga cikin jami’an tsaro ya harba bindiga mai harsashi sama da nufin tsorata matasan, amma sai daya daga cikin harsasan da ya harba ya samu wani mai aikin walda da ke nesa da ofishin APC mai suna Bala, inda ya mutu nan take.

Wani wanda lamarin ya auku a gabansa mai suna Musa Garba, ya shaida wa wakilinmu cewa wanda harsahin ya kashe mai suna Bala dan gudun hijira ne daga garin Wukari  da fadan kabilanci ya sa ya zo gari Bali don samun mafaka.

Kawo lokacin hada wannan rahoto, Sanata Yusuf A. Yusuf bai amsa kiran wayar wakilinmu da sakon tes da yake masa kan wannan lamari ba, amma wani na kusa da shi mai suna Abdullahi Bali ya ce wadanda ke adawa da sababbin shugabannin Jam’iyyar APC a karamar hukumar ta Bali da jihar  ne suka bai wa matasan kudi don su ci mutuncin Sanata Yusuf A. Yusuf.

Ya ce ba gaskiya ba ce cewa an yi yunkurin hallaka Sanata Yusuf domin ba wanda ya taba shi, kuma ya gana da shugabanin jam’iyyar har ma ya bai wa jagoran yakin neman zabensa mota kuma sun bar garin Bali lami lafiya, ba kamar yadda ake yayatawa ba cewa wai a guje Sanatan da ayarinsa suka fice daga garin Bali saboda ruwa duwatsu da matasa suka yi musu ba.

Idan za a iya tunawa dai a garin na Bali matasa sun taba kai wa wani dan Majalisar Wakilai a karkashin APC mai wakiltar mazabar ta Bali da Gassol, mai suna Garba Garba Chede hari lokacin wani taro da ya gudanar.

A wancan lokacin matasan sun yi wa dan majalisar wanka da ruwan leda sannan suka farfasa motocinsa tare da  kwashe babura da kwamfutoci da kudade masu yawa da ya yi niyar raba wa magoya bayansa.

Haka a makon jiya wadansu matasa sun yi wa ayarin sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar Ibrahim EL-Sudi ruwan duwatsu lokacin da ya isa kusa da babban ofishin APC a garin Jalingo don rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihar.

Matasan sun hana Ibrahim El-Sudi da ayarinsa shiga ofishin na APC wanda hakan ya tilasta masa canja hanya zuwa wani wuri daban, inda ya gudanar da rantsar da sababbin shugabanin jam’iyyar a can.

Shugabannin na APC na zargin Hajiya Jummai Alhassan da haddasa hargitsi a cikin jam’iyyar domin na hannun damanta ne aka tsige.

Jummai Alhassan ta shaida wa wakilinmu ta waya cewa tana a Abuja kuma ba ta da hannu kan rigimar da APC ta samu kanta a Jihar Taraba bayan sauke tsofaffin shugabaninta. Ta ce sauke Alhaji Abdulmumini baki a matsayin shugaba a maye gurbinsa da El-Sudi ba tare da an shaida wa baki laifin da ya yi ba, ba daidai ba ne kuma ya saba wa tsarin dokokin APC.

Hajiya Jummai Alhassan ta cewa ita ce ta sharwarci Alhaji Abdulmumini baki ya tafi kotu ya kalubalanci sauke shi da uwar jam’iyyar ta yi, ta ce Babbar Kotu ta hana El-Sudi gudanar da komai sai kotun ta saurari karar da baki ya shigar gabanta.

“Ya kamata uwar jam’iyyar ta sake nazarin matakin da ta dauka domin haka zai kawo cikas muddin dai ana son jam’iyyar ta yi tasiri a zabubbuka masu zuwa. Kuma gwamnatin jihar tana iya amfani da wannan dama ta haifar da rashin zaman lafiya don cimma burin siyasa,” inji ta.

’Yan sanda na kci gaba da gadin ofishin jam’iyyar a Jalingo, inda aka hana bangarorin biyu masu adawa amfani da shi. Kakakin ’Yan sandan jihar Taraba, ASP Dabid Misal wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya gargadi matasa su daina yarda ’yan siyasa na amfani da su wajen kawo rigimar siyasa a jihar.

Bincikin Aminiya ya gano cewa har zuwa yanzu ba wanda aka kama dangane da aika-aikar da matasa ke aiwatarwa da cin mutucin wadansu manyan jam’iyyar ta APC a jihar.