✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar Shugaban kasa a Adamawa na neman tayar da kura

Gwamnatin Jihar Adamawa ta musanta zargin da ake yi mata na hana filin gudanar da gangami a ranar 29 ga Afrilu da Shugaba kasa Goodluck…

Gwamnatin Jihar Adamawa ta musanta zargin da ake yi mata na hana filin gudanar da gangami a ranar 29 ga Afrilu da Shugaba kasa Goodluck Jonathan da Jam’iyyar PDP za su gudanar a jihar. A lokacin da yake yi wa Aminiya bayani ta waya, Kakakin Gwamna Murtala Nyako, Malam Ahmad Sajoh ya ce PDP ta yi musu karya domin ba wani shirin da suke yi don hana gudanar da taron da suke shirin gudanarwa. “Don me za mu hana su gudanar da taron siyasa? A’a su yi abin da suke so, ba wani dalili na hana su wurin taro. PDP dai ta rasa maganar yi ne, kun san duk jihar da suka je suna neman tsokana saboda ba su da ta cewa,” inji su. Ahmad Sajoh ya kara da cewa, domin hada kulle-kulle don kawo tashin hankali a yayin ziyarar Shugaba Goodluck zuwa jihar, yanzu haka akwai tabbacin cewa PDP ta yi hayar yara don su jefi ayarin Shugaban kasar, domin su ce APC ce ta jefe su. Sakataren PDP na Jihar Barista A.T Shehu a yayin da Aminiya ta tuntubeshi ta waya, ya ce gwamnatin jihar ta so hana gudanar da taron PDP domin haka nE ta ce sai an biya amma da suka gan hakan ba zai yiwu ba sai suka hakura. Ya yi watsi da zargin hayar matasa don jifar ayarin Shugaban kasar kuma ya ce suna sane da cewa gwamnatin APC tana ta kulle-kullen ganin ba a kai ga yin taron ba. Ya nemi jama’a su yi watsi da ikirarin da ’yan APC ke yi.