Da Dumi Dumi

Ziyarar shugabannin APC ga Obasanjo ta tada kura

n Shugabannin Jam’iyyar APC lokacin da suka ziyarci Obasanjo.Ziyarar da shugabannin Jam’iyyar APC ga tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ta tada kura a tsakanin magoya bayan Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan da kuma wasu masu ra’ayin sauyi.
daya daga cikin wadanda suka soki ziyarar shi ne Farfesa Wole Soyinka inda ya yi gargadin cewa kasar nan tana neman komawa gidan jiya lura da sabon salon siyasar da aka shiga.
Farfesa Soyinka ya yi gargadin cewa Najeriya tana bukatar aikin ceto ta idan har shugabannin APC za su nemi Obasanjo ya zama daya daga cikin masu ceto ta.
Ya ce a yayin ziyarar daya daga cikin shugabannin APC, Asiwaju Bola Tinubu ya ce APC ta yanke shawarar ceto kasar na kuma tana bukatar Obasanjo ya jagoranci wannan yunkuri. Ya ce, “idan har da gaske Tinubu ya fadi haka, to ina shawartar kowa ya nade kafar wandonsa don aikin ceto Najeriya. Kuma Tarayyar Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Tarayyar Afirka da Majalisar dinkin Duniya da sauran kungiyoyin duniya su zauna cikin shirin ceto Najeriya.”
Wani da ya nemi tsayawa takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti Yarima Dayo Adeyeye ya bayyana ziyarar ta shugabannin APC ga Obasanjo a matsayin “munanfunci da neman mulki ido rufe.”
Adeyeye ya ce “Zuwa wurin Obasanjo, mutumin da suka rika kira da miyagun suna kan ya shiga jam’iyyarsu, shugabannin APC sun nuna ba su da alkibla suna bukatar neman mulki ne kawai ido rufe don bukatunsu na son rai.”
Wani tsohon dan Majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa Alhaji Abba Anas Adamu ya ce Obasanjo ne matsalar kasar nan kuma shi ne matsalar Jam’iyyar PDP, don haka ya bukaci Gwamnatin Tarayya da Jam’iyyar PDP su gaggauta korarsa daga cikin jam’iyyar tunda ya fito fili ya ce shi ne uban Jam’iyyar APC .
Sai dai Jam’iyyar PDP ta kasa ta ce ba ta ji zafin ganawar ta Obasanjo da shugabannin APC ba.
Ta ce tunda tsohon Shugaban kasar ya shaida musu cewa har yanzu shi dan PDP ne babu abin da APC ta samu a ganawar.
Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na kasa na Jam’iyyar, Alhaji Ibrahim Jalo, ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa zai zamo kuskure a zargi Obasanjo da laifi kan ziyarar.
A yayin ziyarar Cif Olusegun Obasanjo ya ce, Jam’iyyar APC ta dauki mataki na farko na sake mayar da Najeriya babbar kasa, kuma ya ce, APC alheri ce ga fagen siyasar Najeriya.
Gwamnoni biyar na PDP da suka sauya sheka zuwa APC su ma sun halarci taron.
Taron dai ci gaba ne na ganawar da APC take yi da bangarori daban-daban na siyasar Najeriya.

Share