✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zurfafawa da tsanantawa a ma’aunin Musulunci (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, Wanda Yake cewa: “Ya ku Ma’abota Littafi! Kada ku zurfafa a cikin addininku abin da ba gaskiya ba,…

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, Wanda Yake cewa: “Ya ku Ma’abota Littafi! Kada ku zurfafa a cikin addininku abin da ba gaskiya ba, kuma kada ku bibiyi son zuciyoyin wadansu mutane wadanda suka riga suka bace a gabani, kuma suka batar da wadansu masu yawa kuma suka bace daga tsakar hanya.”

Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad wanda yake cewa: “Lallai addini sauki ne, babu wanda zai tsananta addini a kansa face ya gallabe shi,” da alayensa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, a yau za mu dubi wani batu ne da ake yawan magana a kansa, wato tsanantawa a cikin addini (GULUWI), wanda ke nufin wuce gona da iri wajen yin wani aiki na addini ko nuna soyayya ko kiyayya ga wani ko wadansu.

A Musulunci ana so mutum ya kasance mai yin komai bisa ma’aunin tsaka-tsaki, kada ya tsananta ya zurfafa kada kuma ya yi sakaci ya watsar. Shi ya sa Allah Yake siffanta wannan al’umma ta Annabi (SAW) da Ummatul Wusda wato matsakaiciyar al’umma. Ma’ana al’ummar da take yin komai tsaka-tsaki ba ta zurfafawa ta wuce gona da iri, kuma ba ta sakaci har ta tozarta addinin.

To, amma kamar yadda malamai suka nuna, Shaidan wanda shi ne babban makiyin dan Adama a kullum yakan yi kokarin raba mutum da addini, ya raba shi da bin hanya madaidaiciya ya raba shi da bin dokokin Allah ta hanyar sakaci da tozarta hukunce-hukuncen addinin.

Idan ya samu nasara ta haka, shi ke nan bukatarsa ta biya, ba sai ya je mataki na gaba ba. Idan kuma bai samu nasara ba, sai ya koma ta wajen da zai sa mutum ya bata ayyukansa wajen zurfafawa da wuce gona da iri. Ma’ana idan mutum mai aikata masha’a da fasikanci ne, sai Shaidan ya yi ta kawata masa wadannan munanan ayyuka ya yi ta aikata barna ya raba shi da hanyar Allah, ta yadda zai samu abokin tafiya wuta. Idan kuma ya ga mutum ma’abucin son addini ne, mai kokari wajen kare dokokin Allah da kawo gyara, sai ya koma ya rika kawata masa cewa ya zurfafa ya wuce gona da iri ya yi kari a kan abin da aka shar’anta masa ko ya tsananta a wasu al’amura domin ya bata masa addini ya raba shi da wannan hali na tsaka-tsaki da Allah Ya siffanta wannan al’umma da ita.

A irin haka ne ake samun kirkirarrun ayyuka na addini da suke kokarin maye gurbin ayyukan da suka tabbata daga wanda ya zo da addinin Annabi Muhammad (SAW). Ko kuma mutum kawai ya dauki tsananin soyayya ko kiyayya ya dora ga wani ya kuma gina kansa a haka.

Ya zamo duk wanda mazhabarsu daya ba, ko kungiyarsu ba daya ba, ko darikarsu ko fikirarsu daya ba, to wancan mutum ba ya da wani alheri a tare da shi. Kuma dan mazhabarsu ko dan kungiyarsu ko darikarsu ko fikirarsu, duk abin da ya aikata daidai ne ba ya taba yin kuskure kullum kuma a cikin alheri yake koda kuwa yana aikata kuskuren.

Wajen sakaci da tozarta dokokin addini akan samu mutane su halatta kusan komai, koda kuwa a fili shari’a ta haramta abubuwan. Sukan fassara nassoshin addini bisa ra’ayi da radin kansu, su soki fassara da fahimtar magabatansu, su nuna su kadai ne suke kan gaskiya. Da haka sai su kwance duk wani kulli na Musulunci har a kai matsayin da komai ya zo daga tunaninsu ko tunanin mustashrikun (masu da’awar su masana Musulunci ne na daga Turawan Yamma wadanda ba Musulmi ba), shi ne addinin.

Sannan wajen zufafawa da wuce gona da iri kuma akan samu wadansu mutane suna haramta abubuwan da shari’a ta halatta da tsanantawa a cikin abin da shari’a ba ta tsananta ba. Da zurfafawar da ta ketare iyaka wajen nuna so ko ki ga wani abu ko wani mutum. Da wannan sai a ga abubuwa sun cukurkude a tsakanin al’ummar Musulmi, har a kai ga zubar da jinin Musulmin ba gaira babu dalili, kamar yadda aka samu a baya inda Khawarijawa suka rika halatta zubar da jinin Musulmi da kuma yanzu da ’yan Boko Haram da dangoginsu suke halatta zubar da jinin Musulmin ko abokan zamansu da ba Musulmi ba, ba tare da wani dalili na shari’a ba.

Allah Madaukaki Ya hana zurfafawa da wuce gona da iri a cikin addini inda Ya ce: “Ya ku Ma’abota Littafi! Kada ku zurfafa a cikin addininku abin da ba gaskiya ba, kuma kada ku bibiyi son zuciyoyin wadansu mutane wadanda suka riga suka bace a gabani, kuma suka batar da wadansu masu yawa kuma suka bace daga tsakar hanya.” (Ma’ida: 77).

Irin wadannan masu zafin rai da zurfafawa a addini sun faro wannan tu’annati ne tun Annabi (SAW) na duniya. Zurfafawa da wuce gona da irinsu ce silar rikita tarihin Musulunci da aukar da yake-yake a tsakanin Musulmi da haifar da rarrabuwa a tsakaninsu da jefa su a cikin mummunan bala’i da kunci.

Malamai sun ce jagoransu shi ne Zul Khuwaisarah Alhurrul Kausi Attamimi,  wanda ya soki Annabi (SAW) a kan wani rabo da ya yi. Ya ce da Annabi (SAW): “Ka yi adalci domin ba ka yi adalci ba.”  Kuma ya ce: “Lallai wannan rabo ba a nufi fuskar Allah da ita ba.” Wannan ya fusata Manzon Allah (SAW) har ya ce: “Kaitonka! Idan ni ban yi adalci ba wane ne zai yi adalci?” Sai Annabi (SAW) ya ce masa shi da mabiyansa yana mai zarginsu: “Daga cikin irin wannan mutum za a samu wadansu mutane da za ku rika raina sallarku a kan sallarsu da azuminku a kan azuminsu da karatunku a kan karatunsu (wato sun fi ku iya su) amma za su fice daga Musulunci kamar yadda kibiya take ficewa daga cikin baka. Wadannan su ne mafiya sharrin halittu a wurin Allah…”

Kuma Annabi (SAW) ya ce: “Wadansu mutane za su bayyana a karshen zamani masu karancin shekaru, masu mafarkan wauta, suna magana da maganar mafificin halitta, suna karanta Alkur’ani amma ba ya wuce makogwaronsu, za su rika ficewa daga addini kamar yadda kibiya take ficewa daga cikin baka, idan kuka hadu da su ku yake su, domin a yakarsu akwai lada ga wanda ya kashe su a wurin Allah Ranar Kiyama.” (Buhari: Hadisi na 3610 da Muslim: Hadisi na 1064).

Don haka Manzon Allah (SAW) ya hana zurfafawa da tsanantawa a cikin al’amuran addini. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Kada ku tsananta wa kawunanku, har a tsananta a kanku. Domin wadansu mutane sun tsananta wa kawunansu sai Allah Ya tsananta musu.” Abu Dawuda ya ruwaito. Kuma ya zo a cikin Buhari cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Lallai addini sauki ne, babu wanda zai tsananta addini a kansa face ya gallabe shi.” Kuma (SAW) ya ce: “Muntani’una sun hallaka… sai dai ya fadi haka sau uku.”

Imam Annawawiy (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Muntani’una sun hallaka: Ma’ana su ne masu tsanani masu zurfafawa da ketare iyakoki a cikin maganganunsu da ayyukansu.” (Sharhin Muslim, mujalladi na 16, shafi na 220).