✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwa ga Gwamnan Jihar Zamfara

Tare da sallama irin ta addinin Musulunci, assalamu alaikum. A matsayina na dan Jihar Zamfara, wanda yake a karkashin jagorancinka, ina son bayyana ra’ayina bisa…

Tare da sallama irin ta addinin Musulunci, assalamu alaikum. A matsayina na dan Jihar Zamfara, wanda yake a karkashin jagorancinka, ina son bayyana ra’ayina bisa niyyarka ta gina sabon Gidan Gwamnatin Jiha, don tabbatar da Zamfara ta kai tsara ta la’akari da irin yadda aka bar mu a baya ta gefen babban gida mallakar gwamnati. Babu shakka wannan nazari ne mai kyau kuma ci gaba ne mai alfanu.

Duk da haka ba zan so in bar garabasar da dokar kasar nan ta ba ni ba ta fadin albarkacin bakina a matsayina na dan kasa. Wato kamar yadda ya zo cikin sashe na 39 na kundin tsarin mulkin kasar nan kasancewa kowane lokaci irinmu masu nazari da sharhi a kan al’amurran yau da kullum ba a rasa mu da sa baki a kan wasu abubuwa mabambanta da suka shafi kasar nan, wani lokacin ma har da wasu kasashen ketare.

Ranka ya dade! Hakika akwai wasu muhimman ayyuka da suka kamata ka yi da suka fi wannan aiki muhimmanci. Niyyar gwamnatinka ta gina katafaren gidan gwamnati wanda zai lashe zunzurutun kudi har Naira miliyan dubu bakwai a bana, a nawa ra’ayi wani babban kuskure ne. Idan muka dubi irin yadda jihar ba ta gama tasowa ba daga cikin babban ƙalubalen da ta fuskanta cikin shekarun baya na tsaro da kuma na ’yan wawura. Dalilin da ya sa nake ganin waɗannan kuɗaɗe sun yi matukar yawa shi ne, kasancewer yanzu haka akwai wasu sassa a cikin jihar da ba su  da wadatattun ruwan sha da wuraren shan magani da kuma uwa-uba wutar lantarki.

A duk cikin kasar nan Zamfara ce kawai jihar da ba ta da jami’a mallakar gwamnatin jiha. Sannan kuma mafi yawa daga cikin ’ya’yan talakawa ba su iya karatu a Jami’ar Tarayya da muke da ita a jihar nan. Saboda rashin abin yi ga shi kuma suna bukatar yin karatu. A ganina zai kyautu a fifita samar da irin wadannan ayyuka a kan wannan aiki na gina sabon gidan gwamnati.

Tun kafin a je ko’ina a cikin babban birnin jihar nan wato Gusau har yanzu ba a samun wadataccen ruwan sha, ballantana a yi maganar ƙananan hukumomi da sauran gundumomi zuwa ƙauyuka. Lallai ne Mai girma Gwamnan Jihar Zamfara a sake nazari a kan wannan lamari, domin kana da matuƙar ƙima da kwarjini a idanun talakawan Jihar Zamfara.

Mun san cewa gyara abin so ne, to amma adadin kudin da wannan aiki zai ci zai bar wani wagegen giɓi a kasafin kuɗin bana, kuma ko bai bar gibi ba kamata ya yi a ce wannan kudi an zuba su ne inda talakawa za su ci gajiyarsu kai-tsaye ganin cewa tattalin arziiin Jihar Zamfara bai da ƙarfin da za a iya fitar da waɗannnan ƙuɗaɗe ba tare da ya girgiza ba, musamman idan muka yi  la’akari da cewa Jihar Zamfara ba ta da wasu manyan hanyoyin da kuɗaɗen shiga ke zuwa, kamar sauran jihohi manya irin su Kano.

Wasu daga cikin ƙananan asibitocinmu suna matuƙar buƙatar kula, musamman yadda za a kawo marar lafiya, amma babu isassun jami’an kiwon lafiya. Sannan hanyoyin karkara sun yi matuƙar lalacewa musamman idan damina ta zo. Wasu hanyoyi ba a iya bin su duk da tarin kasuwannin da ke cikinsu.

Haka fannin samar da ruwan sha wadatacce a yankunan karkara, jama’a na matuƙar buƙatar famfunan tuƙa-tuƙa ko manyan rijiyoyin burtsatse. Don haka ina kira ga Gwamna ya karkato da hankalinsa ya dubi wannan fanni, domin ganin jihar ta samu ci gaba ta kowane fanni, mutanenta su amfana da romon mulkin dimokuradiyya. Allah Ya ba ka ikon ganin wannan ra’ayi nawa, domin a dubi talaka da idon rahama. Ina fatar alheri gare ka, Allah Ya ci gaba da yi maka jagora a mulkinka.

Nura Muhammad Mai Apple Gusau, Dan Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara, 08133376020