✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwa ga Hukumar INEC

Salam Edita da fatan kuna lafiya. A yau ina son ka ba ni dama ne domin in tofa albarkacin bakina bisa yadda gwamnatin Najeriya da…

Salam Edita da fatan kuna lafiya. A yau ina son ka ba ni dama ne domin in tofa albarkacin bakina bisa yadda gwamnatin Najeriya da Jam’iyyar APC ta kasa ke son yin amfani da hukumar zabe (INEC) wajen biyan bukatun kansu ta hanyar shirya murdiya da magudi don karbar jihohin da ake tunanin babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke shirin kwacewa daga gare su. Ko shakka babu an yi walkiya mun gan ku, kuma wannan ba karamin abin kunya ba ne a ce gwamnoninku sun gaza kawo bantensu sakamakon gaza yi wa al’ummar jihohinsu abin a zo a gani da zai sa a sake zabarsu a wa’adi na biyu, amma kuna so ku yi amfani da rashin kammaluwar zabe domin kakaba wa mutane abin da suka gaji da shi.

Saboda daukacin jihohin da aka gaza bayyana wadanda suka lashe zaben gwamnoninsu jam’iyyar adawa ta PDP ce ke kan gaba, shi ne ake neman birkicewa da karfin dawo-dawo, kuma wannan ba karamin ta da zaune tsaye ba ne da kuma gurgunta dimokaradiyyar Najeriya ba. Sannan hukumar zabe kin koma cin gashin APC maimakon cin gashin kanki da ake  yi miki lakabi da shi!.

Daga jajirtaccen dan kishin talaka Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Baure Jihar Zamfara. 09029324453, 07086868025.