✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwa ga Sarkin Musulmi

Assalamu alaikum warahmatullah. Na rasa da wace kalma ya kamata in bude wannan wasika tawa lura da wanda zan so wannan sako ya je gare…

Assalamu alaikum warahmatullah. Na rasa da wace kalma ya kamata in bude wannan wasika tawa lura da wanda zan so wannan sako ya je gare shi ba karamin mutum ba ne a fannoni da dama. Sai dai kuma ina kyautata zaton babu wata kalma da ta fi dacewa in furta maka fiye da ta neman amincin Allah da na yi a farkon wasikar.

Bayan haka, ranka ya dade ina so in fara da jinjina maka bisa ga namijin kokarin da kake yi wa al’ummar da kake mulka sannan in kara taya ka murna bisa baiwar da Allah Ya yi maka ta darewa bisa karagar kakanninka.

Sai dai kuma ina so ka kara sanin cewa shi wannan mulki da Allah Ya ba ka ba karamar amana ba ce kuma abin tambaya ne a ranar tsayuwa. Hakika ba karamin sonka Allah Yake yi ba da Ya ba ka wannan mulki kamar yadda yake fada a cikin littafinSa mai girma cewa “Yana ba da mulki ne ga wanda Ya so…” Ranka ya dade ina so zan dan yi kira ne gare ka, ka dubi irin abubuwan da suke faruwa a tsakankanin al’ummar Musulmin kasar nan.

Hakika ba karamar baiwa Allah Ya yi maka ba da ya zab o ka daga cikin miliyoyin Musulmin da ke wannan kasa Ya ba ka sarautarsu cewa kai ne Sarkin Musilmi, hakika ba karamin abin alfahari ba ne a gare ka da duk  masoyinka, ba wai don ka fi kowa ne Musulmi sanin addinin ba, a’a Ya zabe ka ne don yana son ka zama jagoran Musulmin Najeriya baki daya.

Iya hada kan al’ummar Musulmin kasar nan duk da na san abu ne mai wuya, sai dai kuma ina da tabbacin Allah Yana taimakon dukkan bawanSa da ya yunkuro don ciyar da addininSa gaba.

Ranka ya dade ina so ka kara sanin cewa dukkan al’ummar Musulmin Najeriya kake mulka ba wata darika ba, don haka kowane Musulmi da ke kasar nan yana karkashin jagorancinka ne kuma dole ya yi biyayya gare ka. Ranka ya dade akwai matsaloli da suke yawan faruwa a tsakanin Musulmin kasar nan don haka yana da kyau a ce kana sa baki sosai koda za a ce ka fiye magana. Da ma wannan yana daga cikin aikin shugaba yin magana a kan abin da ya dace.

Ranka ya dade ko kana da labarin yadda ake shigowa garuruwanmu ana satar yaranmu a kai su Kudu a maida su Kiristoci, wadansu kuma ana bin su kauyukansu a ba su kudi kalilan don a samu a canja musu addini? Ranka ya dade don Allah ka hada kwamatin gaggawa da zai binciki yaya aka yi irin wadannan matsaloli suke faruwa sannan a hukunta masu satar yaran.

Ranka ya dade ka tuna dole sai da Musulmi fa kake Sarkin Musulmi, ga shi kuma wadansu suna neman karar maka da jama’a.

Hakika ranka ya dade duk cikin iyaye da kakanni da suka yi mulkin wannan masarauta tun daga kan Sarki Muhammadu Bello wanda ya fara mulki a 1817 har kawo kan yayanka Muhammad Maccido babu wanda ya mulki mutane da suka kai yawan naka duk da cewa kusan kai ne mafi karancin shekaru a cikinsu. Lallai wannan ma ba karamar baiwa ba ce Allah Ya yi maka. Ranka ya dade kana mulkin sama da Musulmai miliyan 60 da ke wannan kasa ta Najeriya.

Ranka ya dade don Allah ina so ka kara yin aiki da kwarewa da dabarun da ka samu lokacin kana aikin soja, wajen hada kan Musulmin kasar nan. Ranka ya dade tashe-tashen hankali sun yi yawa a mafi yawan garuruwan Musulmin Najeriya, musamman a yankin Arewa.

Ka tuna fa kai ne tsohon Kwamandan Dakarun Wanzar da Zaman Lafiya na Kungiyar OAU a Chadi. Har ila yau ka taba zama wakilin Sojin Najeriya a Kungiyar ECOWAS, bayan zama wakili a Rundunar Sojin Yammacin Afirka da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Saliyo. Ranka ya dade a kara duba garuruwan Musulmi akwai matsaloli ta fannoni da dama.  Allah taimaki Sarkin Musulmi, Ya kara maka lafiya  da taimakon talakawa.

Wassalam. K. Bello Kiyawa (0703-252-8895) [email protected]