✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwa Ga Shugaba Muhammadu Buhari (2)

Na san kai kila ka manta, amma ni har yau ban manta da tambayar da kuma amsar da ka ba ni ba, na dai ce…

Na san kai kila ka manta, amma ni har yau ban manta da tambayar da kuma amsar da ka ba ni ba, na dai ce da kai shin ba ka jin ka yi nadamar karbar shugabancin PTF, ganin irin tonon sililin da ake ta yi na cewa ka yi wandaka ko kuma wadansu na kusa da kai sun yi almubazzarranci da dukiyar al’umma a matsayinka na Shugaban PTF? A lokacin nan na san tambayar ba ta yi maka dadi ba, musamman ganin cewa ina daga cikin wadanda ba su amince da ka amshi Shugabancin PTF ba, ina kuma gudun kada ’yan Najeriya su lalata min mai gaskiyar da nake so da kauna ne shi ya sa!

Bayan ka nisa, ka kalle ni, ka ce da ni, aikin Shugabancin PTP kira ne daga kasa don na ba da gudunmawa, kuma in za a sake nemana, in sake ba da gudunmawa zan sake karba, in yi, iya yina. Ma’ana, ba ka yi nadamar amsar wannan matsayi da mukami ba, duk da ce-ce-ku-ce da aka rika yi daga baya.

Wannan tunani ina jin shi ne ya sa ka tsunduma a cikin siyasa daga baya, domin shi ma kamar yadda na auna, kira ne daga al’umma, mabambanta, domin ka sake ba da gudunmawa ga ceto kasar nan daga halin ha’ula’i da ta samu kanta a ciki, musamman daga ‘gurbatattun’ ’yan siyasa da suka yi ta damalmala ta tun daga  1999. Ina da yakinin wannan tunani naka ya ginu ne bisa akidar da kake da ita, ta yin aiki da shugabanci tukuru domin al’umma ba don wani abu da za a samu ba. Sai dai bisa ga dukkan alamu, hada-hadar farfajiyar siyasa da tsarin dimokuradiyya ba naka ko na irinka ba ne, masu kaifi daya, domin siyasa ta gaji fuska biyu da munafunci da son rai da neman abin duniya, ba tare da kishin kasa ko al’umma ba, wanda ina jin suna daga cikin abin da ya sa ka kasa kai gaci cikin sauri ko kuma ka samu tarnaki wajen gudanar da mulkin kasar nan, kamar yadda ka so. Zan dawo kan wannan nan gaba.

Ni abin da ya fi damuna game da irin halin da ka samu kanka a halin yanzu shi ne na rashin sanin ina aka nufa, me za a yi, yaya za a yi, da kuma matakan da suka dace su kasance madafun da za ka yi amfani da su domin kaiwa ga tudun-mun-tsira. Ina kuma jin wannan bai rasa nasaba da yadda ka shiga siyasar da dagwalon da ka bi ka kai ga matsayin da kake a yau. Na san ka sani, idan ba don hadakar jam’iyyarka ta CPC da ANPP da ACN da aka yi a ran 6 ga watan Fabrairun 2013 da kila ba ka kai labari ba, ganin cewa ka daura gyauto don kokowar samun shugabancin kasar nan a baya, akalla sau uku, amma ba a samu ba. Da kuma ka samu wannan damar, na san wannan tsarin ya yi maka dabaibayi, da ya hana maka yin irin yadda ka so, a lokacin da ka so. Ke nan tsarin jam’iyya da dimokuradiyya, ya Shugaba Buhari, da alama bai yi maka kwalliyar da kai da kuma yawancin mutanen da ke matukar sha’awarka kai ga wannan mulki ko matsayi ke bukata ba. Idan na ce ka samu kanka a matsayin wanda ke bisa turbar gaba-kura-baya-siyaki, ina jin ban yi kuskure ba. Kuma wannan ita ce matsalar, duk kuwa da cewa akwai babbar matsalar da ta fi ta, wadda kai ne asasi kuma kai ne ta shafa, kai-tsaye ba wai tsarin da ake gudanarwa ba, shi ma zan karaso gabar nan gaba.

Ina mafita?

Bari in soma da batun tsarin jam’iyya da dimokuradiyya da na yi a baya. A matsayinka na tsohon soja, wanda ya yi mulki irin na kama-karya a zamanin mulkin da ba ruwansa da dimokuradiyya, na san ka yi amanna cewa za ka iya kamawa ka karya a wannan sabon tsarin shugabancin naka, idan damar hakan ta samu, amma da tafiya ta yi nisa ne kila ka gane cewa ashe rawar ba ta daka tsalle ba ce, ta tsayuwa ce, ana dan juyawa, a kuma daidai wannan lokaci ba yadda za a yi a zauna a ki taka rawar, shi ya sa aka shiga mirginawa ko da yaya ne, a tsakanin shekarar 2015 zuwa yau.

To amma Mai girma Shugaban Kasa, kana jin wannan kadai ya isa hujjar da za mu ce komai ya ji dangane da wannan tafiya da aka yi a baya? Shin rashin zamanka wuka da nama a tsarin shugabancin kasar nan shi ne dalilin hana ka yin katabus daga wancan lokaci zuwa yau? Shin dole sai ka yi shugabanci irin na soja ko na kama-karya ne za a samu nasarar bajen kolin ci gaban kasa? Shin gaskiya ne cewa ’yan Majalisar Tarayya ne suke tadiye ka, su hana maka famfalakawa da gudu a daidai wancan lokaci zuwa yau? Shin da gaske ne cewa kana ta kokarin motsawa, amma, wadansu ne da ba sa son mulkinka suka hana maka sakat, shi ya sa abubuwa uku da gwamnatinka ta yi niyyar aiwatarwa don ci gaban kasa; wato tabbatar da tsaro da tayar da komadar tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da almundahana suka gagara kawarwa ko samarwa? Shin hujjojin da masu bibiyar mulkinka, musamman masu mutuwar sonka da tsarin mulkinka suke bayarwa na cewa laifin ba naka ba ne, na wadansu ne, shin hakan gaskiya ne kuwa? Ina tabbatar maka ba gaskiya ba ne, bisa dukkan alkaluman adalci da za a yi amfani da su.

Za mu ci gaba