Da Dumi Dumi

Zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari (5)

Ya Shugaba Buhari, ya kamata ka yi nazari da kyau, ka kuma tambayi kanka ko ta canja zane a wasu sassan gudanar da mulkinka, musamman abin da ya shafi harkar ilimi da kiwon lafiya da tsaro a kasar nan? Shin ba ka san cewa gwamnatin da ka gada ta fi ka kasafta kudade domin inganta fannonin rayuwar al’umma ba, duk da kana cewa ka toshe hanyoyin sata da almundahana, ka kuma samar da asusun bai-daya da ya hana fitar da kudade ba tare da ka sani ba? Shin ina tarin kudin da aka ajiye? Me aka yi da su? Me ya sa abubuwa suka ki canjawa duk da matakan da ka bi na toshe kafafen barna? Abin da ya kamata ka tambayi kanka ke nan, kafin jama’a da tura ta kai bango su bayyana maka!

Shin ya Shugabana! Me ya sa ne kullum na dubi irin hankoron da kake yi na ciyar da kasa gaba, sai in ga tamkar na mai ginar rijiya ne? Dubi samar da aikin yi kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa ta nuna, gwamnatin da ka gada ta Shugaba Jonathan ta samar da ayyukan yi ga mutane kusan miliyan 6 a cikin shekara 5 da ta yi tana mulki, alhali kai a zamanin mulkinka korar ma’aikata ka yi da aka kididdige sun kai miliyan 2 a cikin wata takwas kurum da hawanka mulki! Wannan shi ne ci gaba? Ya Shugaba! Ina son ka natsu, ka yi tunani da kyau. Idan dai ba ka samar da aiki kai-tsaye ba ga jama’ar kasa kamar yadda ka alkawarta, to bai kamata a ce kuma korar wadansu za a yi ba, domin yin haka ba ci gaba ba ne. Ina son ya Shugabana ka rika taka-tsantsan a koyaushe, kada ka rika amincewa da jawaban da wadansu na kusa da kai ke gaya maka game da halin da kasar nan ke ciki, a rika tsananta bincike. Na san kana jin abin da Ministanka na Watsa Labarai ke fada, ina tabbatar maka ba gaskiya yake fada ba, sharata yake faman yi a kullum, Aikin N-Power ba aiki ba ne, dauni ne gwamnatinka ta yi ga wadansu zababbu daga cikin al’ummar kasar nan cikin shekara uku, kuma lallai ya rage radadin talauci ga wadansu, amma ba hanya ba ce ta samar da aikin yi. Shi kuwa bashin Trader-Moni kai da kanka ka sani ba aikin yi ne aka samar ba, kyauta ce gwamnatinka ta yi ga masu rabo. Da ake cewa wai za a maido ta biyan bashi, har wadansu su karu nan gaba, kai da ni mun sani cewa, zuki-ta-malle ce, domin kuwa bashin da aka bayar, ba shaidu, ba a rubuta ba, ta yaya za a tsammaci biya! Ita gaskiya tana nan a fili sai dai in ba ka son ka sani.

Mu koma ga batun darajar Naira da yadda ake ta walankeluwa da rayuwar al’ummar kasar nan. Ya Shugaba! Me ya sa daga hawanka zuwa yau, kimar Naira ta kasa daidaituwa, sai balbalcewa take yi? Ka dai san cewa gwamnatin da ka gada ta bar darajar Dala 1 a matsayin Naira 185, kai kuwa tun hawanka, kullum darajar Naira tana kara zuganyewa ce, Dala 1 kan Naira 315 zuwa sama take! Me ke faruwa ne don Allah? Shin matsalar ta zagon kasa ne da nake ji ana ta yawan yayatawa ko kuwa matsala ce ta durkusasshen tattalin arziki da aka kasa gano kansa bare gindi ko kuwa dai matsalar taka ce da ka kwashi komai da ya shafi gudanar da tattalin arzikin kasar nan ka mika shi ga Mataimakinka Osinbajo, kai ba ka da ruwa-da-tsaki a harkar, sai abin da aka bincina maka? Shin hakan shi ne daidai? Ko alama!

Matsalar tsaro da kariyar rai da al’ummar kasar nan kamar yadda yawancin al’ummar kasar suka sani, a kullum tafiyar hawainiya take yi, kai ka sani, kamar yadda sauran al’ummar kasar nan sun sani, ba a shawo kan matsalar ba, domin har yanzu matsalar Boko Haram, tamkar an kashe maciji ne ba a cire masa kai ba. Lallai an shawo kan wasu gaggan matsalolin tsaro da suka addabi jama’ar Arewa maso Gabashin Najeriya, amma ba a kai karshen matsalolin baki daya ba. Rufe kofa da barawo a cikin gida ya Shugaba, ba hanyar zama lafiya ba ce, sai an sake dubarta da kyau!

Batun sace-sacen mutane domin fansar kai da ya yi kamari a wasu sassan kasar nan da kuma ta’addancin kashe mutane ta fuskar satar shanu da kabilanci ko addini shi ma yana nan kwance, ba a shawo kan batun ba. A kullum mutane suka koka, a maimakon a bi matakin gyara, abin da ya fi tashe daga hukuma shi ne, bihim, sai inda ba a rasa ba. A fito kamar ana yi, a kuma koma a yi gum, kamar ba a damu da rayukan da ake rasawa ba, a duk rana ta Allah.

ADVERTISEMENT

Ya Shugabana Muhammadu Buhari! Na dauki wannan tsawon lokaci ne ina bayyana maka abin da ke cikin raina game da tsarin gudanar da gwamnatinka, ba wai don adawa da neman nuna kasawarka da gwamnatinka ba, a’a, domin ka sani, in ba ka sani ba, cewa shi mulki irin wanda ka samu kanka, ba na dan-ba-ni-na-iya ba ne, ba kuma na wanda ya yi suna ne a fagen dattijanka da rikon amana ba ne kawai, ba kuma mulkin ’yan tsiraru ba ne ko na ’yan uwa da abokan arziki ko kuma mulkin an zabe-ni-ba-kuma-wanda-ya-isa-sai-ni. Mulki ne da ke bukatar tarbace, ba kawai daga masu gudanar da mulki kadai ba, daga dukkan sassan ’yan kasa nagari da masu son cig aban kasa da al’ummarta.

Saboda haka, daga karshen wannan tambihi abin da zan kokarta yi shi ne in kawo wasu shawarwari da nake ganin in an yi aiki da su za su iya kawo sauki daga cikin wasu matse-matsen da ke damun al’ummar kasar nan, insha Allahu.

Za mu ci gaba

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya