✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Albashin N615,000 shi ne abin da ya fi dacewa a Najeriya

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya ce biyan Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi shi ne iya abin da ya fi…

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya ce biyan Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi shi ne iya abin da ya fi dacewa na zahiri a ƙasar.

Joe Ajaero ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels kan dambarwar ƙarin mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

“Naira N615,000 shi ne zahirin abin da ya fi dacewa a matsayin albashi; ba maganar albashi kamar na bayi ba.

“Lissafawa muka yi muka ga abin da zai wadaci ma’aikaci a wannan yanayi na tsadar rayuwa,” in ji shi.

A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta sanar da ƙarin albashi da kashi 25 da kashi 35, ’yan fansho kuma kashi 20 zuwa kashi 28 na abin da ake biya a yanzu.

Sai dai ƙungiyar ƙwadago ta yi watsi da ƙarin da cewa ya yi kaɗan.

Shugaban ƙungiyar ya ce suna samun matsin lamba da ma’aikata a matsayinsu na shugabanni; a daya bangaren kuma gwamnati na zagin su.

Ya ce lissafin da suka yi a kan magadanci mai ’ya’ya hudu a wata guda ya kunshi abubuwa 30, ciki har da wadannan:

  1. Kudin haya – N40,000
  2. Wutar lantarki – N20,000
  3. Ruwa – N10,000
  4. Gas din girki – N28,000
  5. Abinci – N240,000
  6. Asibiti = N50,000
  7. Makaranta = N50,000
  8. Kwasan shata = 10,000
  9. Kudin mota = N90,000