✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wanda ya kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Mande yana daga cikin jagororin ’yan bindiga da suka addabi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna

Daya daga cikin ’yan bindiga da suka kai hari tare da sace fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya shiga hannu bayan shekaru biyu da faruwar lamarin.

Idan dai za a iya tunawa, a shekarar 2022 ne ’yan bindiga suka kai harin bom kan jirgin, suka yi awon gaba da mutane da dama tare da kashe wasu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce dan ta’addan mai suna Ibrahim Abdullahi, ya shiga hannun jami’anta na yaki da masu garkuwa da mutane ne a ranar 12 ga watan Junairu, 2024 a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce, Ibrahim wanda aka fi sani da Mande, ya amsa cewa shi ne shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

ACP Adejobi ya ce, “Mande ya amsa cewa shi ne shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

“Yana cikin manyan ’yan ta’adda irin su Dogo Gide da Bello Turji.

“Yana da hannu wajen yin garkuwa da mutane, ciki har da daliban Jami’ar Green Field.

“Ya kasance yana da hannu a kusan dukkanin sace-sacen da ake yi a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

“Haka zalika da shi aka kai harin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja amma ya gudu.

“Mun yi wa ’yan Nijeriya alkawarin cewa za a kama shi,” kuma yanzu ya shiga hannu rundunar, in ji shi.

ACP Adejobi ya gabatar da Mande tare da wasu mutane sama da 30 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Ya kuma yi nuni da cewa, tsare-tsaren tsaro da aka aiwatar a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sun taimaka matuka wajen samun nasarori.

Ya ce bisa umarnin shugaban ’yan sanda, an tura jirgi sama mai saukar ungulu ya rika yin sintiri domin taimakawa ta sama ga sojojin kasa daga sojoji, ’yan sanda, da sauran jami’an tsaro da ke kan hanyar jirgin kasan.