✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yan Rasha 50,000 a rikicin Ukraine —Rahoto

Rikicin da sojojin Rasha suka yi a yaƙi da Ukraine ya kai ga rasa mutum dubu 50, a cewar wani bincike da aka gudanar.

Rikicin da sojojin Rasha suka yi a yaƙi da Ukraine ya kai ga rasa mutum 50,000, a cewar wani bincike.

Rahoton sashen Rasha na BBC wanda ya yi nazari da  ƙirga mace-mace tun bayan da sojojin Rasha suka mamaye Ukraine da ke maƙwabtaka da ita a watan Fabrairun 2022, ya bayyana adadin a ranar Laraba, tare da cewa adadin mamatan ya ƙaru a shekara ta biyu na rikicin.

Ƙididdigar ta BBC a Rasha ya ambato kungiyar yaɗa labarai mai zaman kanta ta Mediazona da masu aikin sa kai suna cewa  yawan waɗanda suka mutu ya haura dubu 27 da 300 a shekara ta biyu na yaƙin, wanda ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 a shekara ta farko.

Rahoton waɗanda suka mutu a hukumance ɗaya tilo da Rasha ta fitar ya ce a watan Satumban 2022 an kashe sojojinta ƙasa da 6,000.

Binciken ya ce fursunoni 9,000 da aka ɗauka a matsayin sojojin haya na Wagner ko kuma kai tsaye ta Ma’aikatar Tsaro, an kashe su a rikicin.

BBC ta kara da  cewa bayananta ba su bayar da labarin asarar rayuka da aka samu a tsakanin dakarun sa-kai a Donetsk da Luhansk a gabashin Ukraine ba, sannan yawan waɗanda suka mutu a zahiri ya zarce 50,000.

Ukraine ta ce a watan Fabrairu ta yi asarar sojoji 31,000.