✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ce maganin matsalolin Nijeriya — Ganduje

Ganduje ya buƙaci ’yan Nijeriya su mara wa Gwamnatin Shugaba Tinubu baya.

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Umar Ganduje ya ce jam’iyyar za ta samar da hanyoyin magance ƙalubalen da ke addabar ƙasar nan.

Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin babban taron yaƙin neman zaɓe na ƙarshe da miƙa tutocin jam’iyyar APC ga ’yan takarar shugabannin ƙananan hukumomi 11 da aka gudanar ranar Laraba a Gombe.

Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe (GOSIEC) ta sanya ranar 27 ga watan Afrilu domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Ganduje wanda ya gabatar da tutocin jam’iyyar APC ga ’yan takarar, ya ce jam’iyyar a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu na yin ƙoƙari matuƙa wajen tunkarar ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta da kuma ganin Nijeriya ta samu sauyi ga al’umma.

Ya ce, gwamnatin Tinubu na samar da yanayin da ya dace domin ci gaban ƙasa da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

“Tare da kundin tsarin mulki da tsarin mulkin jam’iyyar APC, jam’iyyar ta samu nasarori da dama a matakin ƙasa a mukin shugaba Tinubu.

“Kuma kun ga irin nasarorin da APC ta samu a Jihar Gombe a ƙarƙashin Gwamna Inuwa Yahaya.

“Yanzu a bayyane yake cewa APC ce maganin matsalolin Najeriya,” in ji shi.

Ya buƙaci ‘yan Najeriya da su mara wa gwamnatin shugaba Tinubu da addu’a domin ganin an samu sauyi a ƙasar nan.

Ganduje ya yaba wa Gwamna Inuwa kan yadda ya sanya ajandar sabunta fata nagari na shugaba Tinubu tare da yin aiki tuƙuru domin kawo sauyi a jihar.

A cewarsa, a yanzu Gombe ta zama abin nuni wurin da ake bi wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.

Ya ce, jam’iyyar APC ta ci gaba da alfahari da irin nasarorin da aka samu a jihar Gombe, yana mai bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da suka samu ci gaba a ƙasar nan.

Yayin da yake karɓar waɗanda suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar daga jam’iyyar adawa, Ganduje ya buƙaci mazauna jihar da su zaɓi ‘yan takarar APC.