✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC za ta iya kama Yahaya Bello idan ta so – Bwala

Ya kamata EFCC ta yi amfani da tsarin da ta bi wajen kama Rochas Okorocha a 2022.

Daniel Bwala mai magana da yawun dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a Zaben 2023, Atiku Abubakar ya caccaki Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC).

Bwala ya soki EFCC dangane da ayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Bwala wanda ya yi wannan babatu cikin wani sako da ya wallafa shafinsa na X (Twitter) a ranar Juma’a, ya ce Hukumar EFCC nada duk wata dabara da bayanan sirri da za ta iya kama Yahaya  Bello.

Ya nanata cewa kamata ya yi jami’an EFCC su yi amfani da tsari da kuma dabarar da suka yi wajen kama tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha a shekarar 2022.

Ana iya tuna cewa, a watan Mayun 2022 ne jami’an EFCC suka kutsa kai cikin rufin gidan Okorocha domin kama shi bisa zargin cin hanci da rashawa, bayan shafe sa’o’i shida yana maƙale a gidansa..

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar EFCC ta buƙaci jama’a da su bayar da bayanai game da inda Yahaya Bello yake bayan Gwamnan Kogi na yanzu, Ahmed Ododo, ya tsere da shi daga gidansa da ke Abuja a ranar Laraba.

Lamarin na zuwa ne bayan da a ranar Alhamis hukumar ta yi yunƙurin kama tsohon gwamnan a gidanda da ke Abuja.

Daniel Bwala

Hukumar ta bayyana cewa tana nemansa ne bisa laifukan da suka shafi tattalin arziki na halasta kuɗin haram har naira biliyan 80.2.

Da yake mayar da martani kan wannan batu, Bwala ya bayyana cewa hukumar EFCC na wasa ne da tsohon gwamnan, domin ya ba da zaɓin da za a yi amfani da shi wajen magance lamarin maimakon roƙon ‘yan ƙasar kan neman inda yake.