✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fursunoni 118 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Suleja

Fursunonin sun yi dauki ba dadi da jama'ar garin da suka yi yunkurin kama su

Fursunoni kimanin 118 sun tsere bayan ruwan sama ya rusa katangar gidan yarin Suleja da ke Jihar Neja a daren ranar Laraba. 

Jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a lunguna da sakunan garin Suleja da kewaye a yunkurinsu na kamo wadanda suka tsere.

An ce fursunonin sun tsere daga gidan yairin ne bayan wata iska mai karfin gaske da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya rushe sashin katangar gidan da suke tsare a ciki.

Wani mazaunin garin, Abdullahi Nura, ya shaida wa wakilinmu cewa fursunonin sun yi galaba a kan jami’an da ke gadi, suka tsere ta hanyoyi daban-daban, inda wasu daga cikinsu suka yi ta jifan jama’ar garin da suka yi yunkurin tare su.

Abdullahi ya ce, “Jifan da fursunonin ke yi ya lalata wasu motocin da ke ajiye a bakin hanya a cikin garin Suleja.”

Hukumomin tsaro sun ce an kama uku daga cikin fursunonin a cikin daren Laraba a unguwannin da ke kewaye da gidan yarin.

Am kuma kama wasu da dama da safiyar Alhamis a Unguwannin Rafin Sanyi da Kwankwaso da ke kan hanyar Suleja zuwa Madalla.

Wakilinmu ya yi kokarin yin magana da kwamandan ’yan sandan yankin Suleja, ACP Muhammad Sani Musa, amma bai yi nasara ba, domin bai samu wayar jami’in ba har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto.