✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 a Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano a safiyar Juma’a.…

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano a safiyar Juma’a.

Aminiya ta rawaito cewa akalla mutane 11 lamarin ya rutsa da su, kuma yanzu haka Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Kano na ci gaba aikin ceto domijb da zakulo su.

Mutane biyu daga ciki da aka samu nasarar kubutar da su dai na nan da ransu, kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin ba su agajin gaggawa.