✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotuna: EFCC Ta Gabatar Da Jami’in Kamfanin Binance A Kotu

An ɗage zaman na yau Alhamis saboda Hukumar FIRS ta gaza yi miƙa ƙunshin tuhume-tuhumen da take yi wa Mista Gambaryan.

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC) ta gabatar da Tigran Gambaryan, jami’in Kamfanin Binance a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin damfara.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, manajan Binance a Afirka wanda ya nemi tserewa a kwanakin baya.

Yayin da ake dakon kamo Anjarwalla wanda a makonnin da suka gabata ya tsere, gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin a gurfanar Gambaryan a kotu, ranar Alhamis.

Sai dai Kotu ta ɗage sauraron ƙarar na yau Alhamis saboda Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) ta gaza yi miƙa ƙunshin tuhume-tuhumen da take yi wa Mista Gambaryan.

Wakilinmu da ya ziyarci Kotun ya aiko da hotunan yadda zaman ya kasance kamar haka: