✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar alhazan Kano ta biya N18bn ga NAHCON

An buƙaci hukumar da ta hanzarta bayar da bizar kafin zuwa ranar da za a rufe yin bizar.

Darakta-Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana cewa hukumar ta aikawa Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) sama da Naira biliyan 18 domin shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2024.

Sanarwar da kakakin hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar ta ce, duk da cewa mutane 3,110 sun biya kuɗin aikin hajjinsu, yawancinsu suna jiran bizarsu daga Hukumar NAHCON.

Danbappa ya kuma buƙaci hukumar da ta hanzarta bayar da bizar kafi ranar da za a rufe yin bizar.

Ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Kano na kammala gyara sansanin alhazai kafin a fara jigilar maniyyata.

Darakta-Janar din ya ƙara da cewa, “ba kamar shekarar da ta gabata ba, a  wannan shekarar gwamnati ta samar da dukkan kayayyakin da ake buƙata a sansanin alhazai gabanin gudanar da aikin Hajji domin amfanin maniyyata.”

Da take jawabi, Hajiya Rabi D’nyako Jami’ar gudanarwa a ofishin NAHCON da ke Kano, ta bayyana ƙudurinta na magance ƙorafe-ƙorafen biza.