✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin sama dauke da fasinjoji ya shige daji da su a Legas

Jirgin kamfanin Dana Air ya zame daga kan titinsa sannan ya ci kasa a cikin jeji da fasinjoji

Fasinjojin sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin saman da suka hau ya shige cikin jeji da su a Jihar Legas.

A yayin da ake ruwan sama ne wani jirgin fasinja jirgin mallakin kamfanin Dana Air ya zame daga kan titinsa a filin jirgi na Murtala Muhammad da ke Legas, sannan ya ci kasa a cikin jeji.

Hakan ya sa fasinjojin ficewa cikin gaggawa don tsira da rayuwarsu da kuma guje wa abin da ke iya biyowa baya.

Bidiyon abin da ya faru da fasinjojin suka ɗauka bayan sun tsallake rijiya da baya ya nuna tayar gaban jirgin ta nuntse a kasa a cikin ciyayi.

Zuwa lokacin hada wannan labari dai hukumomi ko kamfanin Dana Air ba su ce komai kan lamarin ba.

Haka zalika babu bayanin ko wani ya samu rauni ko kuma asarar rai ba.