✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan Kotuna Sun Ci Karo Da Juna Kan Kama Yahaya Bello

Manyan kotuna masu daraja daya sun ba da umarni masu cin karo da juna kan kama tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

A ranar Laraba ne labarin samamen da Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello da ke Abuja domin kama shi ya karade gari.

Sai dai daga bisani Gwamnan Jihar Kogi mai ci, Ahmed Usman Ododo ya yi nasarar tserewa da shi bayan ya kawo masa wata ziyara da ake ganin dauki ne a lokacin da dakarun EFCC suka yi wa gidan Yahaya Bello kawanya.

Bayan sumame na EFCC da sulalewa da Yahaya Bello da Ahmed Usman Ododo ya yi, Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya fitar da wani rahoto kan yadda umanin wasu manyan kotuna ke cin karo da juna kan umarnin kama Yahaya Bello.

Wata babbar Kotu a Lokoja Jihar Kogi ta ba da umarnin hana EFCC kama Yahaya Bello, a hannun  guda kuma wata babbar kotu da ke Abuja ta bai wa hukumar damar kamo shi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

Mai shari’a Emeka Nwite, na kotun da ke Abuja, da yake hukunci kan karar da EFCC ta shigar gabansa, ya ce bayan ya saurari jawabin lauyan hukumar, Rotimi Oyedepo, SAN, da kuma karanta kudirin da suka gabatar ya karkata kan cewa EFCC ta gudanar da binciken kamar yadda ta bukata.

NAN ta ruwaito cewa wata babbar kotu da ke zamanta a Lokoja a ranar Larabar da ta gabata dai, ta hana EFCC kama Yahaya Bello da tsare shi da kuma gurfanar da shi gaban kuliya.

Mai shari’a I. A. Jamil, wanda ya bayar da umarnin ya yi Allah wadai da yunkurin tauye hakkin Yahaya Bello, inda a cewarsa “abin a yi tir da shi ne.”

Alkalin, wanda ya yi watsi da bukatar hukumar da ke kalubalantar hurumin kotun, ya ce: “Da wannan umarni, an hana ta EFCC kamawa, tsarewa da gurfanar da wanda ake tuhuma.”

A nata bangaren, Babbar Kotun da ke zamanta a Abuja ta baiwa Hukumar EFCC dama ta kama Yahaya Bello cikin gaggawa da kuma gurfanar da shi a gabanta a ranar 18 ga watan Afrilu.

“Wannan kotu mai girma ta bada ba da sammacin kama wanda ake tuhuma nan take domin gurfanar da shi a gabanta domin fuskantar Shari’a.

“Yanzu kuma an dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga Afrilu, 2024 don gurfanar da shi.” 

Umarnin kotunan da suka ci karo da juna sun zo ne bayan EFCC ta daukaka kara kan umarnin farko.