✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyya: Yadda na fara sa Daso a fim

Haƙiƙa Saratu ƙarshe ya yi kyau. Allah Ya kyauta namu zuwan. Amin.

Haƙiƙa mutuwar Saratu Gidado  ta girgiza mutane da yawa a ciki da wajen ƙasar nan ciki har da ni.

Domin muna tsaka da aikin hada jaridarmu mai fitowa a ranar Juma’a aka soma yada labarin rasuwarta a shafukan sada zumunta da suka karade ko’ina cikin ƙanƙanin lokaci.

Nan da nan muka shiga ƙoƙarin tabbatar da sahihancin labarin saboda yadda ake ƙiƙirar mutuwa a ƙaƙaba wa jaruman Kannywood.

Mutum na farko da na kira don yi wa ta’aziyya a lokacin da labarin ya tabbata shi ne Ali Hamisu Indabawa wanda ya kawo min ita don in sa ta a fim ɗin Feleƙe wani fim dinsa da na rubuta ya kuma sa ni in ba da umarni a ƙarshen shekarun 1990.

Ali Jindos kamar yadda muke kiransa, bai san da rasuwar ba, duk da kusacinsa da ita, domin ya san ta tun tana Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Kaduna (KadPoly) da kuma koyarwar da ta yi a wata makarantar firamare a Kano.

Na yi masa uzuri kasancewar a yanzu yana ɗaya daga cikin hadiman Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a inda yake kula da harkar ɗaukar hoto da yaɗa labarai.

Baya ga cewa mutuwar fuji’a ce, ta faru ne a tsakiyar mako rasuwar ta bayyana ne a lokacin da kowa yake a bakin aiki.

Mutum na biyu da na kira shi ne Auwalu Mohammed Sabo tsohon Furodusan Kamfanin Shirya Finafinai na Sarauniya, wa ga darakta marigayi Aminu Mohmmed Sabo.

Da bai amsa kiran ba, sai na aika masa da saƙon tes na yi ta’aziyya da zimmar sake kiransa a gaba.

Na yi haka ne domin duk matsayi da ɗaukakar da Saratu ta yi a duniya waɗannan mutum biyu ne sila, sai kuma ni da abokin aikina a Kannywood Habibu.

Yadda na fara sa ta a Fim

Mun taru a wurin da za mu soma ɗaukar fim din Feleƙe a Unguwar Hotoro a ƙarshen shekarun 1990, sai Ali Jindos mai fim ɗin kuma mai ɗaukar hoto, bayan mun daɗe muna jiran isowarsa sai ya zo da Saratu, ya gabatar da ita a matsayin sabuwar ’yar wasa da yake so ya sa ta a cikin fim ɗin.

Ni da Furodusa Habibu Sani muka ƙi, kasancewar ba ta taɓa yin fim ba da kuma gudun matsalar da ka iya biyo baya duk da cewa ta taɓa aure ta kuma mallaki hankalin kanta.

 Ali ya gamsar da mu cewa za ta iya kasancewar tana da matuƙar sha’awa kuma malamar makaranta ce baya ga cewa ta daɗe tana bibiyarsa cewa ya sa ta a fim saboda shi kaɗai ta sani a sana’ar a wancan lokaci.

Shi kuma ya yi mata alƙawarin ba zai kai ta wurin kowa ba sai dai ya sa ta a fim ɗinsa, gudun abin da zai biyo baya.

Da ya gamsar da mu, sai na fara gwadata, na ga lallai za ta iya, sai na yi mata gurbi a wata fita tare da marigayiya Amina Garba, wato Mama Dumba da Suleiman Yahaya Bosho, inda ta fito a matsayin ƙawar Hajiya, shi kuma Bosho a matsayin yaron gidanta.

A nan ni ma na ga fiƙirarta kasancewar a nata ɓangaren babu rubutaccen lafazin da za ta faɗa wato komai da ka ta yi shi bisa umarnin da na ba ta.

Wannan ’yar fitowar ce ta sa da Kamfanin Sarauniya ke ɗaukar sababbin jarumai a shirin fim ɗinsa ta je gwada sa’arta, kuma suka ce ba za su sa ta ba kasancewar babu wanda ya san ta kuma ba ta taɓa yin wani fim da zai sa ga su ga ƙwarewarta ba.

Amma da ta ambaci fim ɗin Feleƙe kuma ta ce ni da Habibu Sani ne darakta da furodusa, sai suka sa ta. A nan ta samu sunan Daso daga rawar da ta taka.

Sarauniya na ɗaya daga cikin kamfanonin da suke da taka-tsan-tsan da kiyaye waɗanda suke sa wa a finafinansu a wancan lokaci musamman mata.

Sun kuma yarda su sa ta ce saboda ambatonmu domin duk kamfanin da suke shirin fim a wancan lokaci ƙungiyoyin wasannin kwaikwayo ne ko masu nasaba ne ƙungiyoyin da suka shiga harkar finafinai ka’in-da-na’in, kuma dukkansu a ƙarƙashin kulawarmu ce a Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano.

Ni a lokacin ina ɓangaren kula da finafinai da daukar hoto, Habibu Sani na kula da ƙungiyoyi kai-tsaye da kuma yi musu rajista a hukumar.

Bugu da ƙari mu muka jagoranci shirya horarwa ta farko ga ’yan fim tare da Hukumar Shirya Finafinai ta Ƙasa (NFC) a ƙarƙashin gamayyar ƙungiyoyin UNESCO a 1996.

Bayanin yadda aka yi suka ba ta gurbin kuwa marigayi Ahmed Abdullahi Kabara tsohon dan ƙoroso kuma daya daga cikin abokan aiki a namu kamfanin shirya finafinai na Ƙ Films da muka ba da shi aro ga Sarauniya, shi ya zo mana da shi a matsayin saƙo daga gare su.

Bayan watsar da shirin fim da kuma sayar da kaset Kamfanin Sarauniya sun koma sayar da shayi da indomi, kuma da na samu labarin haka a shekarar 2013 na je don yin rahoto ga jaridar Aminiya.

Bayan hirarmu da marigayi Aminu Mohammed Sabo sai na tambaye shi a game da ’yar dakinsa Daso, ya ce min ai ta zama tamkar ’yar uwa a gare su domin ba ta rabo da gidansa duk shekarun da suka dauka ba sa harkar fim, ta ci-gaba da zumunci da su.

Haka ma Ali Hamisu ya ce a hirarmu lokacin da nake yi masa ta’aziyya.

Ya ce kuɗin da Daso ta samu na farko a fim ɗin Sarauniya sai da ta je gidansa ta yi wa matarsa da ’ya’yansa alheri, kuma tana zumunci da iyalansa duk da cewa sukan daɗe shi da ita ba su haɗu ba.

Ni ma tun daga wancan lokaci wani aiki bai sake haɗa mu da ita ba har na koma aikin jarida kacokam.

Sai dai ina bibiyar ayyukanta na jin ƙai da suke yi tare da Fauziyya D. Suleiman da Zuwairiyya Girie a ƙarƙashin ƙungiyoyinsu daban-daban da suke samun tallafi daga shirin Future Assured na Hajiya A’isha Buhari a lokaci ina aikin rubutu a Tashar Arewa24.

Amma a duk inda muka haɗu a wani sha’ani na ’yan fim cikin raha da girmamawa ta kan ce “Ga tsohon daraktana!” Kuma haƙiƙa takan durƙusa min salo cikin barkwanci. Daga baya na fahimci cewa kusan hakan ya zame mata jiki a mu’amalarta.

Domin a lokacin shugabancin Abubakar Rabo a Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ina cikin kwamitin tantance ’yan fim da ya kafa don yi musu rajista, a yayin zamanmu a hukumar da shigowarta da ganina sai ta juya za ta fita.

Da Shugaban Kwamitin Ibrahim Mu’azu ya yi mata magana, sai ta amsa masa cikin raha da cewa, ita ta gama tantancewa da rajista kasancewar tana da uwa a gindin murhu.

Sai dai duk da hakan an dai yi mata kamar yadda ake yi wa kowa bayan an yi raha.

Haduwarmu ta ƙarshe da ita a Gwammaja ce a rasuwar Aminu Mohammed Sabo. Lokaci guda muka isa gidan kasancewar wannan ne zuwana na farko na yi ɓatan kai, ita da yake ta saba kai- tsaye ta biyo hanya muka bi ta.

Gaisuwarmu da ita da ƙyar aka yi ta saboda kaduwar da ta yi na rasuwarsar domin ta yi jigilar zuwa duba shi a lokacin da yake jinya.

Kwanci-tashi yau tata ta’aziyyar ake yi. Haƙiƙa Saratu ƙarshe ya yi kyau. Allah Ya kyauta namu zuwan. Amin.