✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta dakatar tashoshin talabijin biyu saboda cin zarafin Musulunci

Taliban ta dakatar da gidajen talabijin na Noor da Baryan.

Gwamnatin Taliban ta dakatar da wasu tashoshin talabijin biyu a Afghanistan daga watsa shirye-shirye saboda “cin zarafin addinin Musulunci da na ƙasa”.

Wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu, Khubaib Ghufran ya fitar a wannan Alhamis ɗin na cewa an dakatar da gidajen talabijin na “Barya” da “Noor” a ranar Talata saboda rashin bin ƙa’idojin aikin jarida.

“Suna yin shirye-shiryen da ke haifar da ruɗani a tsakanin jama’a kuma mamallakan tashoshin suna ƙasashen waje,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

“Tashoshin yaɗa labaran na cin zarafin aikin jarida don haka Hukumar ta dakatar da ayyukansu.”

Ya ce, “Mamallakan tashoshin sun ɗauki matsaya a matsayin ‘yan adawa” saboda haka gwamnatin Taliban kuma ta ɗauki mataki “har sai masu tashohin sun zo nan, sun amsa tambayoyi kan zargin da ake yi masu sannan za a iya janye dakatarwar gudanar da ayyukansu.”

Cibiyar ‘yan jarida ta Afghanistan (AFJC) ta sanar da cewa hukumar yaɗa labaran ƙasar ta sha gargaɗin tashar Talabijin ta “Barya” kan yaɗa kalaman da Gulbuddin Hekmatyar wanda yake tsohon shugaban yaƙi ne kuma tsohon firaministan ƙasar ya yi game da gwamnatin Taliban.

“Ita kuwa “Noor” ta samu gargaɗin saboda tana yaɗa kaɗe-kaɗe da kuma fuskokin masu gabatar da shirye-shiryen mata,” in ji AFJC.

Tashar “Barya” mallakin Hekmatyar ɗan Habiburrahman Hekmatyar ne wanda ke zaman gudun hijira kuma mahaifinsa ya ƙara samun sabani da hukumomin Taliban.

“Abin da ba za ku gani daga gare mu ba shi ne shiru,” in ji Khubaib.

Tashar ta “Noor” mallakin Salahuddin Rabbani ce, wanda kuma ke zaman gudun hijira, kuma ya taba riƙe muƙamin Ministan Harkokin Wajen Afghanistan a ƙarƙashin tsohuwar gwamnatin da Amurka ke marawa baya daga shekarar 2015 zuwa 2019.

Mahaifinsa Burhanuddin Rabbani shi ne shugaban ƙasar Afghanistan a shekarar 1990, amma ya gudu daga ƙasar bayan da Ƙungiyar Taliban ta hau karagar mulki a karon farko inda ta yi mulki daga 1996 zuwa 2001.

A shekarar 2011 ne wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe Burhanuddin Rabbani, inda ya bayyana a matsayin jakadan zaman lafiya na ƙungiyar Taliban, tare da bama-bamai a cikin rawaninsa.