✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aiki: Fadar Shugaban Kasa ta kira ’yan kwadago taron gaggawa

’Yan kwadago sun yi barazanar shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani a ranar Talata.

Yanzu haka Fadar Shugaban Kasa na can tana wata ganawa da shugabannin ƙungiyar ƙwadago a Abuja.

Ganawar wadda wakilinmu ya ruwaito cewa am soma ta da misalin karfe 3:25 na Yammacin wannan Lahadin, na gudana ne a ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na shawo kan barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar ta yi.

Bayanai sun ce Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar, Femi Gbajabiamila ke jagorantar zaman tare da wasu ministoci.

Aminiya ta ruwaito cewa, mahalarta taron na sirri sun hada da Shugaban NLC, Joe Ajaero, da Sakataren TUC, Nuhu Toro da takwaransa na NLC, Emma Ugbaja.

Sauran daga bangaren Gwamnatin Tarayya sun hada da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan, Mai bayar da shawara kan sha’anin tsaron kasa, Mallam Nuhu Ribadu, Ministan Kwadago, Simon Lalong, Karamin Ministan Kwadago, Nkeiruka Onyejecha, Ministan Kudi, Wale Edun, Ministan Kasafi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu da kuma Ministar Jin Kai da Rage Radadin Talauci, Beta Edu

A Juma’ar da ta gabata ce wakilan kungiyar kwadagon suka kaurace wa wani taro da Gwamnatin Tarayyar ta kira a Fadar Shugaban Kasa.

A makon da ya gabata NLC da takwararta ta TUC suka yanke shawarar cewa za su tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 3 ga watan Oktoba.

Ƙungiyoyin sun kuma buƙaci rassansu na jihohi da su fara shiri domin soma zanga-zanga ta ƙasa baki-ɗaya.