✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙarancin man fetur ya ƙara ta’azzara a Sakkwato

Gidajen mai ‘yan ƙalilan da ke buɗe na sayar da man kan Naira 900 zuwa Naira 1000 duk lita ɗaya.

Ƙarancin man fetur ya ƙara tsananta a yayin da dogayen layukan ababen hawa suka mamaye ’yan bunburutu a sassan jihar Sakkwato.

Wakilinmu wanda ya zagaya birnin na Shehu a wannan Juma’ar, ya lura cewa gidajen mai da dama na rufe, yayin da wasu ‘yan ƙalilan da ke buɗe ke sayar da man kan Naira 900 zuwa Naira 1000 duk lita ɗaya.

A binciken da wakilinmu ya samo, ana sayar da galan (lita 5) na man fetur a jihar kan Naira 6000 a hannun ‘yan bunburutu.

“Na sayi rabin galan kan Naira 3000 a wajen ‘yan bunburutu bayan bin dogon layi.

“Ban san inda ƙasar nan ta dosa ba. Wannan gwamnati na adawa da talakawa,” in ji wani mai sana’ar acaɓa.

Wani matuƙin babur mai suna Zayyanu Shehu ya ce, ya sayi lita biyar na man fetur a kan Naira 6000.

“Kuma na sami labarin cewa Naira 7000 ne a wasu wurare,” in ji shi.

Wani direban Keke Napep mai suna Abdullahi ya ce, “Halin da ake ciki ya tilasta min ajiye sana’ar tawa da tsakar rana saboda ba zan iya zama a kan layi na tsawon sa’o’i in sayi lita a kan Naira 1000 ba.