✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2019: Yadda Ango Abdullahi ya gwara kan dattawan Arewa

Jagoran Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Ango Abdullahi ya gwara kan dattawan Arewa bayan da ya bayyana cewa kungiyar ta janye goyon bayanta kan sake…

Jagoran Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Ango Abdullahi ya gwara kan dattawan Arewa bayan da ya bayyana cewa kungiyar ta janye goyon bayanta kan sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben badi.

Farfesa Ango Abdullahi ya shaida wa manema labarai a gonarsa lokacin bikin cikarsa shekara 80 a duniya cewa, sun yanke wannan shawarar ce saboda abin da ya kira “Babu wani abin ci gaba da Shugaba Buhari ya yi wa Arewa a kusan shekara hudu na mulkinsa.”

“Shugaba Buhari ya gaza wajen magance talauci da matsalar ilimi a Arewa,” inji Farfesa Ango.

Ya ce Arewacin Najeriya ne dandalin talauci, kuma yankin ne ya dage wajen ganin Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa a zaben shekarar 2015.

Farfesa Ango Abdullahi ya ce “Ba mu yaba da ayyukan da Shugaban Kasa da gwamnonin Arewa suka yi ba a gwamanatin APC. Mun sa ran za a samu canji bayan Buhari ya ci zabe amma mun zuba ido ba mu ga komai ba. Idan ba wani abu ya canja ba, bai kamata a goyi bayansa idan ya sake neman zabe ba.”

Farfesan ya kara da cewa “Idan ma Buhari bai ci ba, wani dan Arewa ne zai ci zaben.”

Ya ce sun dade da yanke shawarar juya wa Buhari baya tun watanni da dama da suka gabata, “Saboda haka ya kamata a ba su notis, za mu fadakar da mutanen Arewa cewa sun gaza saboda haka idan lokaci ya dawo suna neman kuri’a a ki zabensu,” inji shi.

Sai dai wadansu ’yan’yan Kungiyar Dattawan Arewar ta (NEF) da suka hada da Alhaji Sani Zangon da Manjo Janar Paul Tarfa da Kyaftin Bashir Sodangi su karyata matsayin na Farfesa Ango Abdullahi, inda suka ce babu wani lokaci da suka yi zama suka yanke shawarar cewa ba za su goya wa Shugaba Buhari baya ba.

Shi ma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Mista Ameh Ebute, a martaninsa ga kalaman na Farfesa Ango Abdullahi ya ce yankin Arewa zai zabi Shugaba Buhari da gagarumin rinjaye a zaben na badi, inda ya ce jagoran na NEF bai isa ya yanke shawara a madadin Arewa ba.

Mista Ebute ya ce “Ina cike da bakin cikin in fito fili in mayar da martani ga Farfesa Ango Abdullahi kan lamarin da nake ganin mai matukar muhimmanci ne ga zamantakewar yankinmu da kuma daidaituwar Najeriya.”

Ya ce Farfesa Ango Abdullahi masani ne da ake girmamawa kuma dattijo a Arewa da ake kafa hujja da gogewarsa, “Kuma ba mu da wata matsala a Kungiyar NEF saboda muna riko sosai da manyan manufofi da ka’idoji da akidojinta na kasancewa ’yar ba-ruwanmu da wata jam’iyya. Don haka ina tunatar da Farfesa Ango Abdullahi cewa NEF an kafa ta ce a matsayin kungiyar da babu ruwanta da siyasar jam’iyya. Saboda haka cece-ku-cen da suka mamaye jaridu da dama a baya-bayan na da suke cewa ’ya’yan Kungiyar NEF sun juya wa takarar Shugaba Buhari a zaben 2019 da aka jingina ga Farfesa Ango Abdullahi hakika an yi ne da muguwar manufa,” inji shi.

Ya ce hakan ya saba wa ka’idoji da manufofin da aka kafa Kungiyar NEF a kai kuma ya karkace wa manufar da wakilanta suka amince da ita. “Domin bayani dalla-dalla, ina tunatar da jagoran NEF cewa NEF ba ta yi zama ko taro a baya-bayan nan don ta dauki mataki ko matsaya kan kin amincewa ko amincewa da batun sake takarar Shugaba Buhari ko duk wani dan takara da ke neman kujerar Shugaban Kasa ba a zaben 2019. Don haka bayanan da aka jingina ga Farfesa Ango Abdullahi ya girgiza ni sosai. Kuma ina bayyana cewa wuce gona da iri ne kan ’yancinsa na fadin albarkacin baki ya jigina ra’ayin kashin kansa ga kungiyar, wadda ba ta tare da tunaninsa kan maganar da ya yi,” inji Ebute.

A martanin Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) ta bayyana kalaman na Farfesa Ango Abdullahi kan sake zaben Shugaba Buhari, a matsayin na kashin kansa amma ba da yawun mutanen Arewa ba.

Sakatare Janar na Kungiyar ACF, Mista Anthony Sani ne ya bayyana hakan a zantawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce su ba su da alaka da kungiyar Dattawan Arewa da Ango Abdullahi yake wakilta a kan wannan matsayi.

Kungiyar ta ACF ta ce Ango Abdullahi, ba ya da wata alfarmar da zai wakilci al’ummar Arewa a kan sake zaben Shugaba Buhari, “Mu a matsayinmu na Kungiyar Kare Muradun Arewa, mun nesanta kanmu da kalaman Ango Abdullahi kan sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma babu ruwanmu da wata kungiya wai ita ta dattawan Arewa da Ango Abdullahi yake magana da yawunta” inji shi.

Mista Anthony Sani ya ce tun farko an kirkiri kungiyarsu Ango Abdullahi ne domin ta zama kishiya ga “Kungiyarmu ta ACF saboda haka ba mu yi mamakin kalaman Ango Abdullahi ba, kuma hanyar jirgi daban ta mota daban, ba ruwanmu da matsayin na kungiyar su Ango Abdullahi ta Northern Elders Forum,” inji shi.

Mista Anthony Sani, ya yi kira ga ’yan Najeriya su yi watsi da maganganun da Ango Abdullahi ya yi kan Shugaba Mubammadu Buhari. “Tun a jiya (ranar Litinin) da ya fadi wadannan maganganu wadansu daga cikin dattawa kamarsa da ke wannan kungiya ta NEF suka fito karara suka soki kalamansa,” inji shi.

Injiniya Khailani Muhammad, Shugaban ‘A Kasa A Tsare,’ na Kasa na Shugaba Buhari, ya yi watsi da ikirarin na Farfesa Ango. Ya ce su Farfesa Ango sun yi haka ne don kansu ba da yawun mutanen Arewa ba, “Sai don abin da Atiku zai dauka ya ba su,” inji shi.

Ya ce Shugaba Buhari yana iya kokarinsa, domin ba lokaci daya ake yin gyara ba, sai an dauki lokaci.

Injiniya Khailani ya ce “Idan su da ke kiran kansu dattawa sun damu da matsalolin Arewa me ya sa ba su tashi tsaye ba wajen an tayar da masaku da masana’antun da suka durkushe a yankin?”