✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai fa’ida a kasuwancin kayan marmari – Tukur Mailemu Tukur Mailemu mai sayar da kayan marmari ne a Kasuwar ’Yan Lemu da ke Haliru Abdu,…

Akwai fa’ida a kasuwancin kayan marmari – Tukur Mailemu

Tukur Mailemu mai sayar da kayan marmari ne a Kasuwar ’Yan Lemu da ke Haliru Abdu, bayan Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kebbi. A tattaunawarsa da Aminiya, ya ce akwai fa’ida a kasuwancinsu:

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

Yaushe ka fara sayar da kayan marmari?

Na kai kimanin shekara 15 ina yin wannan kasuwanci a nan Kasuwar ’Yan Lemu da ke Haliru Abdu a Birnin Kebbi. Kuma ina zaman lafiya da kowa da ni da ma’aikata da sauran abokan zama baki daya.

Duk kayan nan, a nan muke gyara su idan an kawo mana su daga Kurmi ko wadanda aka kawo mana su nan daga gonakinmu da ke yankinmu kamar kankana da karas da makamantansu da ake shukawa a nan Arewa. Sai mu wanke don a saye su da tsabta wato ciki lafiya, baka lafiya.

Yaya kuke da hukomomin gwamnati?

Suna hana wadanda suka karya doka ne, amma mu muna kokarin kiyayewa. Domin muna kwashe shara mu zuba a buhu mu adana har a zo a kwashe, don haka ba ma tara shara.

Kuma ma’aikatan lafiya kusan kowane lokaci suna zagayowa suna duba yadda muke tsabtace kayan marmarin, ba mu sayar da wanda ya lalace. Duk wanda ya lalace ko dabbobi ba mu bari su ci, sai dai mu zubar. Kuma gaskiya akwai fa’ida a kasuwancin.

Me da me kuke sayarwa?

Wannan kasuwa muna sayar da kayan marmari da kayan lambu ko da rani ko da damina. Muna sayar da namu da aka saba da su da wadanda ba a saba da su ba, wato irin na Turawa da na kasashen China. Wasu kuma ana kawo mana irin ne kamar irin albasar kasar China wacce muke yafawa mu yi ban-ruwanta har ta girma mu debo mu gyara mu sayar. Muna ce mata Chai domin albasa ce wacce ba ta da jan kwallo irin namu sai dai kawai tana da lawashi, sauran ba su da suna a Hausa kamar su koriyanda, falak ko falalan alayahho, hendibe da ba’ale da sauransu.

Idan mutum ya zo neman abin da babu yaya kuke yi?

Idan muna da wurin da za mu samo sai mu karbi lambar waya, idan an samu mu kira mutum mu sanar da shi an samu ya zo ya karba.

Kuna yin kwangila zuwa otel ko manyan gidajen abinci ko gidajen masu hannu da shuni?

Gaskiya ba ma yi sai dai mutum ya zo ya saya, domin muna gudun wahalar biyan kudi da sauransu, domin mu ba manyan ’yan kasuwa ba ne.

Yaya kuke yi lokacin damina?

Muna da wurin da muke fake ruwa, amma yawancin kayan ai ba ruwansu da ruwan sama, sun fi son ruwan sama ya wanke su, ruwan saman yakan rage mana aiki.

Kun kai mutane nawa a wannan wuri?

Muna da yawa, za mu kai kimanin 25 domin kowa da bangarensa har da masu yin shayi da masu tuwo da masu gasa nama da sauransu.

Ko kuna da wata bukata ga gwamnati?

Kwarai da gaske muna kara kira ga Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya tallafa mana domin mu kara inganta harkokinmu, domin ya san mu har nan yakan zo mu gaisa.