✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina sanya siyasa kan matsalar tsaro – Pasali

Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zabe ta Shugaban Kasa Muhammad Buhari (Buhari Campaign Organization) ta Kasa. A tattaunawarsa da wakilinmu…

Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zabe ta Shugaban Kasa Muhammad Buhari (Buhari Campaign Organization) ta Kasa. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce akwai rashin tunani da siyasa ga masu cewa Buhari ya sauka daga mulki kan matsalar tsaro:

Me za ka ce kan kira da wadansu ke yi ga Shugaban Kasa Buhari ya kori shugabannin tsaro saboda kasa magance matsalar tsaro da take damun kasar nan?

Abin da nake son mutane su gane Shugaba Buhari tsohon soja ne, don haka ba bako ba ne kan abin da ya shafi sha’anin tsaro. Kuma abin da mutane ya kamata su gane abubuwa sun tabarbare lokacin da ya karbi shugabancin kasar nan. Domin a lokacin ana maganar Boko Haram, sun kwace garuruwa da dama daga hannun jami’an tsaro. Yanzu duk wadannan abubuwa sun zama tarihi, sai dai hare-haren da ake kaiwa ne suka rage.

Kuma duk wuraren da aka samu irin wadannan rikice-rikicen da Najeriya ta shiga a baya, ba abu ne da za a iya kawar da shi a lokaci daya ba.

Idan aka tuna a shekarun baya an yaki ’yan Taliban a kasar Afghanistan, amma har yau akwai ’yan Taliban ba a iya kawar da su ba. Don haka abin da ya shafi yakin sunkuru, wanda ba mutum ne zai fito gaba- da-gaba a yi yaki da shi ba, abu ne da zai yi wuyar kawarwa a lokaci guda, dole sai dai a bi a hankali.

Kuma gaskiyar magana duk da ’yan majalisa sun yi kira kan a cire shugabannin tsaron kasar nan, dole ne mu yi kira ga Shugaban Kasa ya sake duba wannan al’amari, saboda idan aka ci gaba da nanata abu, watakila akwai wani abu na damuwa, musamman ganin shugabannin tsaron nan, lokacinsu na yin ritaya ya yi.

Amma maganar tsaro kowa ya san yadda aka san kasar nan, lokacin da Shugaba Buhari ya karbi mulki zuwa wannan lokaci da muke ciki, an samu nasarori masu yawa.

Don haka da dama masu matsa wa Shugaba Buhari ya kori shugabannin tsaron nan, sun sanya siyasa ce kawai musamman jam’iyyar adawa ta PDP da ta mayar da harkar tsaron kasar nan siyasa. Abin har ya kai ga Sanata Abarebe yana ce wa Shugaban Kasa Buhari ya sauka daga mulki. Yadda kullum PDP ke fitowa da ’yan tsirarin mutane suna zanga-zanga, kan wannan al’amari ya nuna cewa akwai siyasa a ciki.

Don haka babu shakka akwai son zuciya kan kiraye-kiraye na a kori shugabannin tsaron. Domin  duk wanda aka kawo sai an fadi illarsa.

Kuma shugabannin tsaron nan, sun yi bakin kokarinsu kan yadda suka samu kasar nan. Mutane ba sa iya zuwa masallatai da coci-coci da kasuwanni da makarantu da asibitoci da wuraren aiki. Ai duk wadannan sojoji ne suka yi wannan kokari, aka samu nasarar magance wadannan abubuwa.

Kuma maganar tsaro, magana ce da ta shafi kowanne dan Najeriya. Kowane dan kasa yana da hakki kan tsaron kasa.

A zamanin da Turawa suke mulkin kasar nan, idan abu ya faru a unguwa ko bako kuka gani ya shigo muku unguwa, kun san akwai bako a unguwar, domin sai an je wajen mai unguwar an tambaya daga iya ya fito kuma me ya kawo shi wannan unguwa. Wannan aiki da muka watsar shi ne ya dada kawo mana tabarbarewar tsaro a kasar nan. Saboda haka dole ne al’umma kowa ya ba da gudunmawarsa kan harkokin tsaro.

Ba yaki ake yi da wata kasa ba. Duk masu aikata wadannan laifuffuka a cikin unguwanni suke. Mutane sun san wadanda suke aikata wadannan abubuwa a unguwanninsu. Muna da shugabannin unguwanni muna da kungiyoyin matasa a unguwanni irin wadannan ne ya kamata a karfafa wa gwiwa wajen lura da abubuwan da suke faruwa a unguwanninmu.

Mece ce mafita kan wannan al’amari?

Mafita ita ce kowane Gwamna shi ne shugaban tsaro a jiharsa. Don haka kowane Gwamna ya  tsaya ya kafa harsashin wayar da kan mutane kan harkokin tsaro. A nemo masana kan harkokin tsaro su wayar da kan mutane. Domin a kowace al’umma an san fitinannun cikinta, sarakuna da hakimai da dagatai da masu unguwanni sun san duk masu tayar da hankali.

Shi ya sa na ji dadin matakin da Gwamnan Jihar Filato Mista Simon Lalong ya dauka a ’yan kwanakin nan na sanyawa a kama shugabannin wuraren da aka samu rikici.

Wane kira kake da shi ga gwamnati da al’umma game da lamarin tsaro?

Na farko shi ne  jama’a su zamanto suna sanya ido kan harkokin tsaro  a kasar nan, idan suka yi haka za a samu nasara. Shi kuma Shugaban Kasa da gwamnati, su tsaya su ji shawarwarin jama’a. Idan aka ji koke-koke sun yi yawa, ya kamata a duba domin a dauki mataki.