✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika yi wa gwamnoni da sarakuna gwajin miyagun kwayoyi – Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bukaci a samar da wata doka da za ta tilasta sarakuna da gwamnoni da sauran masu…


Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bukaci a samar da wata doka da za ta tilasta sarakuna da gwamnoni da sauran masu rike da mukaman siyasa su rika gwajin miyagun kwayoyi.

Sarki Muhammadu Sanusi ya yi wannan kira ne a lokacin bude tarom wuni biyu da Majalisar Dattawa ta shirya a birnin Kano kan yadda za a magance matsalar shan miyagun kwayoyi da ke addabar al’umma  yau Litinin.

Ya ce, “Idan muka fara nuna wannan misali, matasa ’yan baya za su fahimci cewa idan suka yi tu’ammali da miyagun kwayoyi, babu shakka za su takaita damarsu ta zamowa shugabanni. Bai kamata ’yan sanda da sojoji da sauran masu sanya kayan sarki maza da mata su rika shan miyagun kwayoyi ba.”

Sarkin ya ce a shirye yake a yi masa gwajin miyagun kwayoyi a yunkurin da yake yi na ganin an magance matsalar a jihar.

A cewarsa, matsalar shan miyagun kwayoyi ta shafi kusan dukan iyali a Arewa. “Gaskiyar lamari shi ne yawancin ’ya’yan masu hali da ke tu’ammali da miyagun kwayoyi sun tashi ne sun gani a gidajensu,” in ji Sarkin na Kano.